Batanci Ga Annabi : Asarar Da Kasar Faransa Ta Fara Shiga ~ Dr. Prof Mansur Sokoto
Wannan wani rubutu ne da shehin malami Dr prof Mansur Ibrahim sokoto ya fara wanda Zai kawo muku irin asar da wannan kasar ta shiga da tsananin rayuwa kan kalaman na batanci ga fiyayen halitta.
Wannan shine farkon rubutun shi wanda yayiwa taken “karshen faransa”
“Karshen Faransa 1
Ba zan manta wani conference da muka yi ba a kasar Ghana a 1997 a birnin Nyakrom wanda ya ba mu damar muka je ziyara a Cape Coast, ta Central Region, kudancin Ghana.
A Cape Coast Castle muka ga irin mummunan ta’addancin da Dutch suka yi wa yan Afrika tun kusan shekaru 500 da suka gabata. A ranar kusan kasa bacci na yi saboda abinda idanuna suka gane mani. Azaba wadda – a nan dai duniya – mutum ba zai taba iya suranta ta ba. Bakaken Amurka suna kuka suna share hawaye duban halin da aka shigar da kakanninsu – wadanda galibinsu an kamo su daga gonakinsu – kafin a aika su a matsayin bayi zuwa kasashen waje.
Daga wannan ranar na daina sauraron gidan Rediyon Dutch har inda yau take magana. Ba ni ko son in ji muryar Dutch Velle ko akan hanya ne saboda tsananin kyamar da ta kullu a rayuwata kan wadancan mutane.
Irin haka ne a yau na ji ga baki daya ba ni jin dadin sauraron gidan Rediyon Faransa. Ya kuwa za ayi in ji dadin sauraron tasharsu alhalin suna wulakanta martabata tare da cin zarafin maigidana da sunan yanci!
Yanzu babban kalubalen da na yaki zuciyata akai shi ne, duk turarukan da nake amfani da su wadanda kullum suke caccakar tattalin arzikina yan Faransa ne. Kowace kwalba daya ta fi gangar man fetur tsada – kamar yadda firaministan Indiya ya ce. Kuma daga yau, in sha Allahu na bar su barin mantuwa.
✍️ Mansur Sokoto
19 R. Awwal 1442
5 Nuwamba 2020.”