Kannywood

Ba adalci a shari’ar Naziru Sarkin Waƙa, inji Nabraska

FITACCEN jarumin barkwanci, Alhaji Mustapha Badamasi (Nabraska), ya yi tsokaci kan shari’ar da ake tafkawa tsakanin fitaccen mawaƙi Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa) da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, ya ce idan za a shekara dubu ana yin wannan shari’a, to abin da ake tuhumar Naziru da shi dai ba gaskiya ba ne.
Artabun Naziru da hukumar daɗaɗɗe ne. Tun a bara ta kama shi ta maka shi a kotu bisa tuhumar cewa ya saki wasu waƙoƙi biyu ba tare da izinin ta ba. Daga baya aka bada belin sa.
Ko a lokacin, da yawa magoya bayan mawaƙin sun yi iƙirarin cewa hukumar ta kama shi ne saboda bambancin ra’ayin siyasa, abin da ita hukumar ta ce ba haka ba ne.
Kwatsam, kwanan nan kuma sai aka sake komawa kotu, inda aka tsare Naziru Sarkin Waƙa a bisa zargin ya kasa cike sharuɗɗan beli. Bayan ya kwana a gidan waƙafi, washegari aka ba shi sabon beli a bisa wasu tsauraran sharuɗɗa. A wannan karon ma, magoya bayan sa sun ce duk siyasa ce shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya ke amfani da ita.
Ɗaya daga cikin masu irin wannan ra’ayin shi ne Nabraska, wanda aminin Sarkin Waƙar ne. Nabraska, wanda wasu ke kira da Sharu Mustapha Nabraska, ya na taka muhimmiyar rawa a cikin wannan shari’a, musamman wajen karɓo belin Naziru.
Bayan sun karɓo belin mawaƙin na kwanan nan, wakilin mujallar Fim ya tattauna da Nabraska kan wannan badaƙala da ake ganin ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
A tattaunawar sa da mujallar Fim, jarumin ya danganta badaƙalar da ƙaddara, ya bada tarihin shari’ar ta Naziru sannan ya faɗi ra’ayin sa.
Nabraska ya soma ne da bayyana cewa, “Kusan komai da ƙaddarar da Allah ya ke sauko wa bawan sa. Wannan wata magana ce wacce da an fara yin ta a wata kotu, daga baya kuma sauyin aiki ya samu wannan alƙalin da ya ke gudanar da shari’ar, ya bar wannan kotun.
“Aka kuma ɗauko maganar aka kawo ta wata kotun daban, wanda shi kuma alƙalin da aka kawo wa shari’ar ya ce shi sai ya fara bibiyar ta tun daga farko tunda maganar yanzu aka kawo masa, ba wai ɗorawa zai yi daga inda wancan ya tsaya ba.”
Nabraska ya ci gaba da cewa: “A can baya ma ni ne wanda na karɓi Sarkin Waƙa da hannu na a waccan kotun ta baya da mu ka bari, amma duba da an ɗauko an sake kawo wa wata kotun daban, sai alƙalin ya bayyana cewa shi fa ya karya wancan belin da aka yi na shi Sarkin Waƙa da na karɓa, inda kuma ya gindaya nashi shi ma ga yadda zai saka belin kamar yadda ya gindaya wasu matakai, wanda kuma an bi wannan matakan.
“To Allah da ikon sa kuma kafin ɗaya daga ciki ya kammala, wannan mai shari’ar aka ce ya tashi. Aka yi ruwa aka yi tsaki don ganin an ga mai shari’a, amma mai shari’a ya yi ɓatan dabo, duk da dai mun yi ƙoƙarin kiran sa har ta waya amma wayoyin nasa duk a kashe.”
Mujallar Fim ta tambayi Nabraska shin bayan Naziru ya kwana a hannun hukuma wane hoɓɓasa su ka yi wajen ganin an sake shi?
Sharu Mustapha Nabraska ya amsa da cewa: “E, ai ka san kowanne tsuntsu kukan gidan su ya ke yi. A wannan lokacin tunda an kai shi ya kwana, aka sake dawowa washegari, kuma kowa ya na iya bin matakai irin nasa da yadda zai iya. Haka mu ma mun bi matakai irin namu da yadda za mu iya, kuma Allah cikin ikon sa mai shari’a ya sake dawowa washegari ya zauna, kuma aka yi dukkanin mai yiwuwa aka kuma bada belin mai girma Naziru Sarkin Waƙa.”
A game da irin sharuɗɗan da kotun ta gindaya a kan Naziru kafin a sake shi, Nabraska ya ce: “Daga cikin sharuɗɗan akwai mahaifi ko ƙanin mahaifi ko wan mahaifi, wanda hakan ba ta samu ba. Akwai babban wan sa, shi ne Misbahu M. Ahmad, kusan shi ya tsaya.
“Sai kuma kwamandan Hisba na uku. Akwai Wakili daga yamma ko gabas ko kudu ko arewa. Su kuma waɗannan sharuɗɗai da mai shari’a ya sa ko ya gindaya, su na kama da kusan duk hukuncin da ya saka a wannan matakai.
“Matakai ne wanda su ke da alaƙa da aikin gwamnati, kuma yau ko da wasa aka ce mutum ya na adawa da gwamnati ko ya na rigima da ita, to za ka ga duk irin matakin da aka sa, in dai akwai ma’aikacin gwamnati a gurin, mutum ba zai yarda ya sa hannun sa ba domin in ya sa akwai yiwuwar za a iya cewa ko dai ya bar aikin sa ko kuma ya rasa wani abu a cikin aikin nasa tunda har zai iya sa hannu.”
Da Fim ta tambayi Nabraska yadda su ka yi da sharaɗin kawo kwamandan Hisbah a matsayin mai beli, ganin cewa ma’aikacin gwamnati ne, sai ya ce, “Ka ga kai ma a matsayin ka na ɗan jarida ka ce kwamandan Hisbah ya na aikin gwamnati, ka ga ko ni ne kwamandan Hisbah, in dai aikin gwamnati na ke yi, ba zan yarda na sa hannu ba.
 
Mujallar Fimmagazine ta kara da cewa Misali, in dai za a danganta abin da rigima da gwamnati ake yi, ka ga ba zan yarda in shiga cikin wannan rigimar ba. To kuma ka ga wannan ya na ɗaya daga cikin abin da alƙalin ya sa. Don haka al’umma da masu karatu su za su kalli abin ta fuskar adalci aka yi ko rashin adalci aka yi?”
Nabraska ya ƙara da cewa, “Duk abin da ya ke gaban kotu dole a saurara a ji hukuncin da kotu za ta yanke. Mun dai san idan za a shekara dubu ana wannan shari’ar, shi abin da ake cajin Naziru da shi, ko menene ma, ba gaskiya ba ne. Duk abin da ake tuhumar sa da shi ba gaskiya ba ne, tsakani da Allah.”
A ƙarshe, Nabraska ya yi bitar laifin da ake tuhumar Nazirun da shi. Ya ce: “Waƙoƙi ne dai guda biyu. Waƙoƙin kuma shi kan sa wanda ya kai shi gurin (wato Afalallah), tun kafin ya zo gurin aka yi waɗannan waƙoƙin aka kuma sake su.
“In an ce waɗannan waƙoƙin ba a tantance su ba, ai ni na jagoranci waƙoƙi kusan guda uku ko guda huɗu waɗanda ba a tantance su ba, kuma sun fita, kuma an yi bidiyon su, ciki har da ‘Masu Gudu Su Gudu’.
“‘Masu Gudu Su Gudu’ ina ɗaya daga cikin waɗanda su ka bada gudunmawa; kai, in ana yin uba a ciki ma, ni uba ne a cikin ‘Masu Gudu Su Gudu’, amma babu wanda ya tantance ta, babu inda aka bayyana ga shaidar ta an duba. Ka ga abin sai al’umma su kalla su ga cewa adalci ne ko rashin adalci ne aka yi? Son zuciya ne ko ba son zuciya ba ne ba? Na yi ra’ayin ka ne ko ban yi ra’ayin ka ba ne dalilin da ya sa ka yi min haka? Ko kuma don ba ka ƙauna ta ne ka yi min haka? Kai, ko dai don ka na so ka nuna wa duniya ka fi ƙarfi na ne ka yi min haka? Kowanne da kalar da zai ɗauki fassarar abin da ake nufi da wannan.
“Abin da ya ke faruwa da Naziru, kai ba ma iya Naziru kawai ba, akwai Sunusi Oscar 442, Alan Waƙa da kuma Sadiq Zazzaɓi, kusan duk haka ta yi kama da kasancewa da su; ko wanne ya na da kes a kotu, ba wai bai da kes a kotu ba.
“Amma a ƙarshe ka ga shi Ala da ya ɗauki abin ya kai Babbar Kotun Tarayya, ka ga ai shi ya ci nasara, aka ce wannan abin ƙarya ne, babu shi, kar kuma a sake tuntuɓar sa a kan wata maganar waƙa. Ka ga kuma ai ba a yi ba har yau.”
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button