Addini
Audio : Jinin Abduljabbar Kabara Kano ya halatta a gaban kotun Musulunci
Mallam Abubakar Sani Madatai, ya fitar da wannan clip da na saka, wanda a ciki, ya yi wa Abduljabbar Kabara raddi absa miyagun lafuzzan da yake saka kan annabi Muhammad (SAWWW)
Ba dadin saurare, amma tun da ya yi kuma yana da’awar wai soyayyar annabi ma yake koya wa jama’a, to dole a tona asirinsa, kuma dole manya su tsaya su ga an yi abin da ya dace akan wannan mutum.
Wallahi ko Imanuwal Makaron na Faransa, bai saki irin lafazin da Abduljabbar Kabara yake saka akan manzon Allah ba.
A saurara da hakuri, kuma wallahi karya yake, bai isa ya kawo irin abin da ya furta ba, kamar dai yadda ya gaza kawo audion nan da ya yi wa wani dan Tijaniya kage!