Labarai
Allah yayiwa Mahaifin Margayi Sheikh Albani zaria Rasuwa
innalillahi wa innaa ilaihi raji’unn
Allah Ya karbi rayuwar Mahaifin margayi Sheikh Albaniy Zaria wato Malam Adam wanda ake yiwa lakabi da Baba Danjuma Dattijon albarka wanda ya haifowa duniyar Musulunci gwarzon Malami shahidi Insha Allah Sheikh Albaniy Zaria
Majiyarmu ta samu wannan labari daga shafin datti assalafy,malam Adam Ya rasu dab da asuba bayan yayi fama da rashin lafiya, zuwa an jima kadan da misalin karfe 9 na safe za’a yi masa jana’iza a gidansa dake ‘Yan Awaki Muchiya Sabon Garin Zaria
Muna rokon Allah Ya gafarta masa
Allah Ya kyautata makwancinsa
Allah Ya hadashi da ‘dansa Malam Albaniy Zaria a gidan Aljannah tare damu gaba daya