Kannywood

Akan Kashe Mutanen Borno Ran Jaruman Kannywood Ya Bace Sunyi Martani Mai zafi

Labari marar dadi sai fitowa suke a yakin arewa wanda babu dadi wanda ake yiwa al’umma arewa kashin gola kamar ana kashe kiyashi wanda jaruman Kannywood.
Wanda shahararren mawakin Nazir m Ahmad yayi martani mai zafin akan shuwagabani inda yake cewa:
Anya ko shugabanni sun fahimci mai ake nufi da hisabi kuwa? Ko dai suna shakku ne akan hisabin?? Akwai wuta akwai aljanna fa


 
Wanda nan take babban jarumi kuma furodusa falalu dorayi yayi Martani mai zafi irin wannan kashin gila da ake yiwa yan uwanmu musulmi wanda nan take ali nuhu ya sake sanya wannan rubutu falalu dorayi ma’ana duk ra’ayin su daya .
 
 
 
Ga abinda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
 
“Akwai tsananin tashin hankali ace kullum da ka Farka daga bacci sai kaci karo da labarin kashewa, sacewa, ko kone garuruwa a Arewa.
Rayukan Al’umma sun zama kamar ran kiyashi, su kuma wadanda Alhakin kula da rayukan da dukiyar Jama’a yake hannunsu sun zama magen LAMI.
Abin bacin rai in dai ta tasu zamu jira domin suyi wani abu to sai dai mu mutu da takaici.
Yaku Shugabanni da masu rike da madafan ikon Arewa. Ko shirya ranar qiyama sai kun zo da bayanin filla-filla gazawarku.
Shugabannin arewa sun gaza,
Allah ka bamu nagari,
masu kishin Al’ummar su.
Allah mun tuba, Allah ya ka kawo mana karshen wannan masifa.
#ZabarmariMassacre
#SecureNorth
#SecureNorth
#falaludorayi
#falaluadorayi”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button