Kannywood

Abin da ya sa na ɗora ɗa na, Sani Freiiboi, kan turbar nishaɗantarwa – TY Shaban

FITACCEN jarumi T.Y. Shaban ya bayyana cewa ya ɗora ɗan sa Sani a kan turbar sana’ar nishaɗantarwa ne saboda ya lura ya na da fiƙira a fagen waƙa.
Shaban ya yi kira ga iyaye da su ma su lura da inda kowane ɗa nasu ya fi karkata a basira, su ɗora shi a kan hanya.
Shaban ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da mujallar Fim ta yi da shi kan shirye-shiryen sa na fitar da sabon fim ɗin sa mai suna ‘Tauraron Ɓoye’ wanda ya shirya a ƙarƙashin kamfanin sa na Bluesound Multimedia.
A fim ɗin, ya haɗa jarumai daga ƙabilu daban-daban na sassan ƙasar nan har ma da ƙasashe masu maƙwabtaka da Nijeriya.
An fara haska fim ɗin a gidan sinima na Filmhouse da ke ‘Ado Bayero Mall’ a Kano a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2020, kuma za a ci gaba da nuna shi har zuwa ranar Alhamis mai zuwa.
Dandazon ‘yan kallo a wajen haska fim ɗin a ‘Filmhouse Cinemas’ a Kano
Babban ɗan TY Shaban, wato Sani TY Shaban, wanda ake yi wa laƙabi da Freiiboi Shaba, ya na daga cikin jaruman fim ɗin, kuma shi ne ya rera waƙoƙin da ke ciki.
Sani yaro ne da Allah ya ba fiƙirar waƙa, musamman a fannin gambarar Hausa, wato hip hop. Haka kuma jarumi ne a Kannywood.
A game da yadda aka yi Sani ya zama mawaƙi, mahaifin sa ya labarta wa mujallar Fim cewa: “Na yi mamaki da na ga Sani ya taso ya na waƙa. Ban taɓa tunanin cewar Sani zai yi waƙa ba saboda ni ma kawai gani na yi ya fara waƙa.
“Kuma wani abu da zai ba ka mamaki shi ne cewar shi Sani ma mahaifiyar sa ce, tunda ita ce ta ke zama da su a gida, ita ce ta ja hankali na a kan cewar in ɗau yaron nan in je in gwada shi a situdiyo saboda ta ga alamar ya na da baiwar waƙa. To ka ji dalilin da ya sa na san cewar ya na ma da baiwar waƙa.
“Kuma wani abu da zai ba ka mamaki shi ne cewar shi Sani ma mahaifiyar sa ce, tunda ita ce ta ke zama da su a gida, ita ce ta ja hankali na a kan cewar in ɗau yaron nan in je in gwada shi a situdiyo saboda ta ga alamar ya na da baiwar waƙa. To ka ji dalilin da ya sa na san cewar ya na ma da baiwar waƙa.
“Kuma na yi ƙoƙarin da zan yi domin in taimaka wa ‘career’ sa; tunda jahili ba ya waƙa; ka ga dole in taimake shi a kan wannan baiwar.”
Jarumin ya ce, “A fannin karatu kuma na sa shi a makaranta fitacciya kuma ina kashe kuɗi mai yawa, ba wai a kan Sani ba shi kaɗai, har da ragowar ‘ya’ya na ga baki ɗaya domin samar musu da ilimin addini da na zamani domin cigaba.
“Duk kuma wanda ya ke tare da ni ya san irin ƙoƙarin da na ke yi a kan ilimin yara na, saboda ilimi shi ne garkuwar ko waye a rayuwa.”
Bugu da ƙari, Shaban ya ja hankalin al’umma game da ‘ya’yan su, inda ya ce, “Babban kira da zan yi ga al’umma shi ne idan mun haifi ‘ya’ya, kamar yadda mu ka san sunan wannan Musa, sunan wannan Muhammad, Fatima Zahra da waye, to mu gane cewar Zahra fa ba daidai ta ke da Fatima ba, akwai abin da Allah ya ƙunsa wa Fatima bai ƙunsa wa Zahra ba.
“A matsayin ka na uba, kai ne za ka zauna ka gane cewar Zahra ga gun da ta fi ƙarfi, Fatima ga gun da ta fi ƙarfi, bari in taimaki Fatima a kan wannan gurin kuma in taimaki Zahra, ba in ɗauko son rai na ba na ɗora a kan ‘ya’ya na a kan sai kaza na ke so su zama, wanda kuma ba shi ba ne abin da Allah ya dasa musu a zuciya.”
Haka kuma ya ce, “Mu a arewacin Nijeriya mu na da matsalar abin da ake kira a turance ‘career development’, wato rainon yara tun daga matakin farko a ɗora su kan wani tafarki wanda ya zo daidai da baiwar da su ke da ita, kuma a taimaka musu kan wannan baiwar domin a samu ingantacciyar al’umma a bar alfahari gobe. Don haka na yi wani abu ne sadaƙatuj jariya zuwa ga al’ummar mu.”
Shaban ya ce shi da ma an haife shi ne da harkokin nishaɗi, “na kuma fara harkar finafinai tun ina da ƙananan shekaru. Kimanin shekaru 15 na fara harkar nishaɗantarwa a wani guruf wanda ya haɗa da ni da Sani Danja da wasu mutum uku a ciki, wanda kuma aƙalla na kwashe shekara sama da ashirin a cikin masana’antar.”
Game da fim ɗin ‘Tauraron Ɓoye’, ya ce saƙon da ya ke son isarwa shi ne na farko iyaye, gwamnatoci, attajirai da malamai su gane cewa mu na da matsala a wannan ɓangare na rainon yara masu baiwa, kowa kuma ya gane a fara tun daga gida a matsayin ka na uba, ka gane ‘ya’yayen ka guda biyar kowanne akwai irin baiwar da ya ke da shi, sannan wane taimako za ka iya ba shi domin ya cimma burin sa a kan wannan baiwar.”
Ana hira da Samira Ahmad a wajen kallon ‘Tauraron Ɓoye’
A kan irin ƙalubalen da ya fuskanta wajen shirya fim ɗin, Shaban ya ce: “Babban ƙalubalen da na samu shi ne akwai jarumai da dama da na kawo cikin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, akwai daga Nollywood ɗin kudancin Nijeriya, akwai daga Ghana, akwai kuma daga Lebanon, to haɗa waɗannan jaruman a Jihar Kano da Abuja shi ne babban ƙalubale da na fuskanta da kuma musamman ƙalubalen kawo kayan aiki nagari wanda na ɗauko su daga wata uwa duniya, wanda aka zo nan aka rasa su waye za su sarrafa waɗannan kayan aikin. A haka sai da aka ƙara ɗauko wani daga kudancin Nijeriya aka haɗa shi da su sannan aka yi ƙoƙarin yin aikin da ya kamata a yi.”
Amma kuma akwai nasarori. Jarumin ya ce, “Babbar nasara ta ita ce na shirya wannan fim ɗin domin mutane su zo su kalla don su ɗauki darasi kuma su fuskanci cewar ga taimakon da T.Y. Shaban ya yi domin al’ummar sa, musamman Jihar Kano wanda da su na ke alfahari.”
Shi dai TY Shaban, haifaffen unguwar Birged ne a cikin birnin Kano.
Ya yi karatun firamare a ‘Bridgade Special Primary School’, da na sakandire a ‘Kano Teachers College,’ sannan ya yi babbar sakandire a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Stadium da ke Kano.
Daga nan kuma ya je Kwalejin Koyon Aikin Malanta ta Gwamnatin Tarayya da ke Bichi a Jihar Kano. Da ya gama kuma ya koma ya karanta ‘Advanced Diploma in Public Administration’ a ‘Kano State Polytechnic,’ sannan a nan ya yi babbar diflomar sa.
Jarumin, wanda kuma shi ma mawaƙi ne, ya bayyana cewa ya sha karo da ƙalubale a rayuwa. Ya ce: “Yau sama da shekara ashirin da fara fim ɗi na. Ina da tarin ƙalubale wanda kuma a ciki akwai wanda aka yi kuka, akwai kuma wanda aka yi maganin shi, akwai wanda ma ake gum da baki, da dai sauran su.”
Sadiq Mafia, Umar Gombe da TY Shatan a wajen kallon fim ɗin
Idan ba a manta ba, shi ne ya auri fitacciyar jaruma Samira Ahmad a matsayin matar sa ta biyu, su ka haifi ‘ya guda ɗaya kafin su rabu.jaridar Fimmagazine ce ta wallafa wannan rubutu a shafinta munka kawo muku.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button