Kannywood

Abin Da Ya Dace Ku Sani Game Da Lamarin Matar Auren Da Ta Fito A Bidiyon Wakar Jahata Ce Ta Rarara

Marubucin nan Indabawa Aliyu Imam a facebook shine na farko da bayana wannan labari kuma shine ya sake zuwa da wasu bayanai guda goma sha biyu wnada ya kawo wanda ya kamata ku sani wanda dai har yanzu ba’a ji ta bakim mawaki rarara ba.
Ga abubuwan da yakamata ku karanta
1. Ka’idar hukumar tace fina-finai ta jahar Kano babu darakta ko frodusa da zai sanya wacce ba ta da register da hukumar tace fina-finai ba, yin hakan saba doka ne.
2. Hukumar tace fina-finai ta na yin register ne ga wacce aka tabbatar cewa ta shigo film da yardar iyayenta ko wani magabaci nata gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.
3. An sha samun matsaloli daga matan da suka gudo daga wajen iyayensu ko daga dakunan mazajensu suka zo ake saka su a film, sai daga baya a gane gaskiya, gudun hakan ne ya sa aka kirkiri tsarin register don tabbatar da cancantar kowacce ‘yar wasa.
4. Wannan matar aure da ake magana ba wai ta fito ne a ‘yar rawa ko wani abu mai kama da haka ba, ta fito ne a matsayin tauraruwar waka.
5. Hukuma kwanaki ta kama Naziru sarkin waka an kaishi Kotu wanda har gidan ‘dankande sai da ya bakunta bisa rashin kawo wakarsa a tace masa.
6. Shin Ali Nuhu da Dauda Rarara a matsayinsu na Darakta da Frodusa na wannan shiri mai ya sanya suka yi amfani da wacce ba ta da register da hukumar tace fina-finai?
7. Rarara ya na da cikakkiyar register da hukumar tace fina-finai, shin bayan kammala bidiyon wakarsa bai mikawa hukumar tace fina-finai ta tace ba kamar yadda yake a dokance wanda har aka kai Naziru Sarkin waka Kotu bisa hakan.
8. Idan ya baiwa hukuma don ta tace ko mai yasa hukuma ta lamunce sakin bidiyo alhalin akwai wacce ba ta da register a cikinta?
9. Bani da hannu sam a cikin wannan rikici, ban kuma dauki bangare ba. Shi mijin wannan matar dan unguwarmu ne kuma shi ya same ni ya labarta min ya kuma nemi da na bayyana labarin, inda na yi bincike na tabbatar da sahihancin labarin sai na fitar da shi don hukuma da sauran daraktoci su gyara su daina saka wacce ba su da masaniya game da ita.
10. Mijin matar nan babu abin da ya tauye mata na hakkinta, rana guda ya dawo gida ya neme ta ya rasa, babu irin cigiyar da bai yi ba bai sami inda take ba, ashe wurin su Ali Nuhu da Dauda Rarara ta tafi suka saka ta a bidiyonsu na waka.
11. A karshe mijin wannan mata mai suna Abdulkadir Inuwa tuni ya debi lauyoyi wanda ya ce za su tsaya masa wajen kwato masa hakkinsa na karya dokar masana’antar Kannywood da aka yi aka sanya matarsa a bidiyon waka ba tare da an yi mata register ba, wacce register ce ke tabbatar da amincewar iyayenta ko danginta a dokance.
12. Muna fata hukumar tace fina-finai za ta shiga tsakani tayi kokarin samar da sulhu game da wannan dambarwa tun kafin lamarin ya zo ya rincabe.
Allah ya kyauta ya baiwa maigaskiya Nasara.
Indabawa Aliyu ImamMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button