Kannywood
Yayi Amai Ya Lashe : Ali Nuhu Yabi Sahun masu Zanga zanga #SecureNorth
Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, ya yi amai ya lashe sakamakon a yanzu ya shiga zanga-zangar #SecureNorth, inda a baya ya ƙi shiga zanga-zangar kan wasu dalilai nasa.
A baya dai, dalilin da ɗan wasan ya bayar na ƙin shiga gangamin da aka shirya na jawo hankalin mahukuntan Najeriya kan rashin tsaron da arewacin kasar ke fama da shi ya janyo masa matukar suka a shafin Twitter amma duk da haka, tauraron ya shaida wa BBC cewa shi ko a jikinsa.
Tun a farkon mako ne wasu al’ummar arewacin kasar suka soma gangami domin yin tur da irin halin tabarbarewar tsaro da yankin ke ciki.
Sai dai da alama a yanzu jarumin ya bi sahun masu zanga-zangar inda ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Instagram na goyon bayansu.