Labarai
Yanzu – Yanzu : Gwamnatin nigeria ta haramta Zanga-zanga
Bayan karban shawarwari daga masana tsaro da masu iko da tsaron Kasa suka isarwa shugaba Buhari, gwamnatin Nigeria ta haramta cigaba da gudanar da zanga-zangar ENDSARS a fadin kasar Nigeria gabaki daya
Dokar haramcin ya fara aiki daga yau Alhamis, Gwamnati ta bawa jami’an tsaro umarni da su dauki matakin kamewa da tarwatsa duk wata rundina ta masu gudanar da zanga-zangar ENDSARS
Masu zanga-zangar ENDSARS an yi musu abinda suke so amma sunki denawa, iskancin nasu yana neman wuce iyaka, umarnin da aka bawa jami’an tsaro su tarwatsasu yayi daidai
Yaa Allah Ka mana maganin duk wani tsageri da mai mugun nufi akan zaman lafiya da tsaron Kasarmu Nigeria Amin