Labarai

Yadda Buhari Ya Kasafta Wa Kowacce Ma’aikata Kudin Ta A Cikin Kasafin Shekarar 2021

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce an ware wa manyan ayyuka naira Tiriliyan 3.85 a kasafin kudin 2021.
A – An ware wa Ma’aikatun gwamnatin Tarayya naira Tiriliyan 1.80
B – Naira biliyan 745 don ayyukan da zasu taso
C – Naira biliyan355 na ayyukan taimako da tallafi
D – Naira biliyan 20 domin shirin samar da gidaje
E – Naira biliyan 25 domin asusun inganta matasan Najeriya
F – Naira 336 don ayuukan wasu ma’aikatun gwamnati 60
G – Naira biliyan 247 wasu ayyukan gwamnati da za su taso na cigaba
H – Naira biliyan 710 don ayyukan da za a yi da basuka na hadin guiwa.
Buhari yace kasafin manyan ayyuka na bana ya fi na bara da naira Tiriliyan 1.15.
Ya ce za a fi maida hankali wajen kammala ayyuka masu yawa da aka fara a baya ne maimakon kirkiro sabbi.
1 – Za a kashe wa fannin Wutan lantarki naira biliyan 198.
2 – Ma’aikatar Ayyuka naira biliyan 404
3 – Ma’aikatar Sufuri naira biliyan 256
4 – Ma’aikatar Tsaro, naira biliyan 121
5 – Ma’aikatar Ayyukan Gona da Raya Karkara, Naira biliyan 110
6 – Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, naira biliyan 153
7 – Ma’aikatar masana’antun da Kasuwanci, naira biliyan 51
8 – Ma’aikatar Ilimi, naira biliyan 127
9 – Hukumar UBEC, naira biliyan 70
10 – Ma’aikatar Kiwon Lafiya, naira biliyan 132
11 – Hukumar Raya Yankin Neja Delta, naira biliyan 64.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnagtin sa na gina tituna a karkara har 331 a fadin kasar nan.
Buhari ya bayyana haka da yake gabatar da kasafin kudi na 2021 a zauren majalisa ranar Alhamis.
Ya kara da cewa wadannan hanyoyi da ake ginawa da gyara duk sai da aka tabbata hanyoyi ne da za su taimaka wa manoma.
Wasu daga cikin manyan hanyoyi da gewamnatin Buhari yi yanzu sun hada da titin Ilorin-Jebba-Mokwa-Birni Gwari, Lagos-Ibadan Expressway, Enugu-Onitsha da sauran su.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya gabatar da Kasafin Kudin 2021 a majalisar tarayyar Najeriya ranar Alhamis.
Buhari ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 13 kasafin 2021.
Gwamnati ta ɗora ƙudurin kasafin kuɗin na 2021 kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 379 da kuma mizanin gangar man fetur guda a kan dala 40, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 1.86 a kullum.
.
Daga Comr Abba Sani PantamiMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button