Kannywood

Tsugune Ba Ta Ƙare Ba: Rushe SARS ba alkhairi ba ne – Hamisu Iyan Tama

Shahararren Fardusa na fina-finan Hausa, kuma ɗan siyasa a jihar Kano Alhaji Hamisu Lamido Iyantama ya bayyana cewa har yanzu tsugunne ba a ƙare ba game da rushe sashen da ya ke yaƙi da ƴan fashi da makami da kuma manyan laifuka na rundunar ƴan sandan ƙasar na wato SARS ba.
Hamisu Iyantama ya bayyana haka ne a shafinsa na fasebuk, inda masu bibiyar sa a shafinsa su ka kafsa muhawara tare da bayyana ra’ayinsu game da hakan.
“An samar da hanyar tsaro mai inganci amma wasu sun yaki lamarin”
“Bance babu kura-kurai ba amma da an yi musu kwaskwarima ya fi a rushe su gaba daya”
“Babu wani sashe da babu matsala amma amfanin sashen yafi matsalar amfani ga al’umma” in ji Hamisu Iyantama
Hamisu Iyantama ya ce an daɗe ana kashe ƴan uwan mu a jihohin Katsina da Borno da Zamfara da Sokoto da kuma jihar Kaduna.
Ya ƙara da cewa an cigaba da kashe mutane a jihohin Benue da Yobe da kuma Niger da sauran jihohi musanman a yankin arewacin Najeriya, amma babu wasu waɗanda suka fito suka yi zanga zanga domin gwamnati ta kawo mafita, amma wai yanzu har da daga ƙasashen ƙetare ake taya masu zanga zangar.
“Ku yi tunani ku nutsu, ku yi hattara, ku tuna halin da mu ke ciki arewacin Najeriya da kuma irin amfanin da jami’an tsaro su ke bayarwa”
Alhaji Hamisu Iyantama ya ƙara da cewa ban ce babu matsaloli b, ko a lokacin da ba SARS ana samun Matsaloli tsakanin ƴan ƙasa da jami’an tsaro.
Majiyarmu ta samu daga dokin karfe,haka zalika Iyantama ya ce wasu sun yi dogon tunani an kashe kuɗaɗe da ɓata lokaci wajen kafa su, amma lokaci ƙanƙani wasu sun zo sun ruguza.
A cikin makon jiya ne dai babban sufeton ‘yan sandan ƙasar nan Mohammed Adamu ya sanar da soke rundunar yaki da ‘yan fashi da makami wato SARS, bayan jerin zanga-zanga da ake gudanarwar a wasu jihohin ƙasar nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button