Kannywood

Tsaron Arewa: Ali Nuhu ya sha caccaka a wajen ‘yan Najeriya saboda rashin shiga zanga-zanga

Shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya sha suka a wajen yan Najeriya da ke amfani da shafin Twitter.

Hakan ya biyo bayan dalilin da jarumin ya bayar na kin shiga cikin zanga-zangar rashin tsaro a yankin arewacin kasar.

Sai dai kuma Ali Nuhu ya bayyana cewa ko kadan hakan bai dame shi ba, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

A farkon makon ne dai wasu mutanen arewa suka soma zanga-zanga a kan halin rashin tsaro da yankin ta tsinci kanta a ciki.

Har ta kai sun kirkiri maudu’i mai taken #SecureNorth, wato a kawo tsaro a Arewa, domin jan hankalin gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari kan irin ta’asar da ‘yan bindiga da masu satar mutane da ma mayakan Boko Haram suke ci gaba da yi.
 
 

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da matasa yankin kudanccin kasar ke kira ga rushe rundunar yan sandan SARS, inda gwamnati ta amsa kiran nasu ta kuma rushe ta.

A wata hira da ya yi da gidan rediyon DW Hausa, Ali ya bayyana cewa wasu daga cikin arumai suna tsoron shiga irin wadannan gangami ne saboda ba sa so a dunga zaginsu.

“Wasu lokutan, kai a matsayinka na jarumi in za ka shiga wata maganar, sai ka ga kamar shisshigi za ka yi wa mutane.

 
 

“Ka je Twitter, a nan ne za ka ga an saka taurarin Arewa a gaba ana zaginsu, a kushe su, a yi musu wulakanci yadda rai yake so. Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane suke ja baya-baya ba wai ba sa son shigowa ba ne.”

Sai dai kuma wannan furuci nasa ya fusata mabiya Twitter inda suka yi sharhi:

Wani mai suna @alamin_ghost a shafin ya ce: “Arewa mu farka don muna da buri wanda shi ne tabbatar da tsaro a Arewa sannan mu kawar da rashin tsaro. Ku manta da Ali Nuhu. Allah na tare da mu.”


 

@__usyy ya ce: “Dan Allah ku kyale Ali Nuhu a yanzu. Sukarsa a wannan lokaci zai janye hankulanmu daga ainahin fafutukarmu. Kada mu sauya alkiblar abunda muke nema.”

@_Sufy2 ya ce: “Ali Nuhu Kannywood ya ce ba zai shiga kowani zanga-zanga a arewa ba saboda sukar Twitter. Shin hakan na nufin bai damu da rayuwar mutanen da ke kallon fina-finansa ba? illa abunda ya fi iyawa shine zama dan aiken Ahmed Musa.”

Da yake yin raddi kan masu sukarsa a Twitter, Ali Nuhu ya bayyana cewa ko a jikinsa kmar yadda sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

“Ba na yin abu don in burge mutane,” in ji Ali Nuhu.

Jarumin ya ci gaba da cewa yana tausayin masu wannan fafutuka saboda shi yana yin abin da yake ganin ya kamata ne.

Da yake magana game irin kudaden da ya bai wa wasu mabiyansa domin su ja jari, Ali ya ce“Ku je shafina na Instagram ku ga abin da na yi.”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button