Labarai
Sufeto Janar Ya Bada Umarnin Janye Ƴan Sandan Dake Kare Manyan Ƙasa (Hoto)
Advertisment
Sufeto Janar Ya Bada Umarnin Janye Ƴan Sandan Dake Kare Manyan Ƙasa
Shugaban ƴan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye ƴan sanda masu kare lafiyar manyan ƙasar nan.
Ya umarci janye dukkan ɗan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a faɗin Najeriya a yau Laraba.
Kawai Gidajen gwamnatoci, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai kaɗai aka amince a basu kariya.