Labarai

Shugaban Kasar Faransa Ya Shelanta Yaki Da Addinin Musulunci ~ Datti Assalafy

Kwanaki kadan da suka gabata, wani Malamin makaranta a Kasar Faransa ya nuna zanen hoto na batanci ga Manzon tsira Annabi Muhammad (SAW) wa daliban makaranta da yake koyarwa
To shine sai aka samu wani matashi wanda mahukuntan Faransa sukace Musulmi ne ya yiwa Malamin makarantar hari da wuka, ya kashe Malamin ya guntule kansa, kafin mutumin ya gudu ‘yan sandan Faransa sun harbeshi, sunce wai asalinsa ‘dan Kasar Rasha ne daga yankin Musulmin Checheniya
Guntule kan Malamin ya jawo zazzafan zanga-zangar yahudu da nasara a Kasar Faransa, shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana kashe Malamin a matsayin harin ta’addanci daga Musulmai, daga nan sai gwamnatin Faransa ta fara tuhumar manyan Malaman addinin Musulunci na Kasar Faransa suna kamasu, sun zargi wani babban Masallaci a dalilin shafin Masallacin na facebook ya wallafa bidiyo na Malamin makarantar lokacin da yake nunawa dalibai zanen batanci ga Manzon Allah suka fadi adireshin makarantar da Malamin yake karantawa kafin a guntule kansa
To bayan da aka kashe Malamin, sai Masallacin ya cire posting din, ita kuma gwamnatin Faransa sai ta dauki matakin rufe Masallacin kawai saboda sunyi posting suna nuna bacin rai akan cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Malamin makarantar yayi, kuma masu lura da Masallacin ba su da hannu a kisan Malamin
A halin da ake ciki yanzu, shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron yana tsanantawa addinin Musulunci sosai tare da jaddada goyon bayansa ga ‘yan uwansa yahudawan Faransa masu yiwa Manzon Allah batanci, wannan ne dalilin da yasa ‘dan kishin Musulunci shugaban Kasar Turkiyya daya daga cikin horarrun sojojin daular Usmaniyya Sheikh Recep Tayyib Erdogan yayi kira da a dubi kwakwalwar shugaban Faransa Emmanuel Macron, domin abinda yake yiwa Musulunci da Musulmai a Kasar faransa ya nuna alamar yana da tabin hankali
Bayan da shugaba Erdogan ya fadi wannan maganar ga Macron, ashe hakan ya bata masa rai, shine a jiya shugaban Faransa Macron ya janye jakadan Kasar Faransa dake Kasar Turkiyyah, wato ya yanke hulda da alakar Diplomasiyyah tsakanin Faransa da Turkiyyah saboda kalmar da shugaban Turkiyyah Erdogan ya fadi a kansa
Kar ku manta fa jama’a, Emmanuel Macron bayahude ne, yana da mugun nufi akan Musulunci da Musulmai, baya la’akari da dunbin yawan Musulmai da suke Kasar Faransa, da gangan suke tsara batanci wa Annabi (SAW) a gidan jaridarsu ta Charlie Hebdo domin su tayar da fitina a duniya, idan Musulmi sun dauki fansa sai su fake da wannan su yaki Musulunci
Allah Ka haramta wa Emmanuel Macron cikar burinsa a kan Musulunci
Allah Ka amintar da ‘yan uwa Musulmin Faransa daga makircin wannan matashin bayahude Amin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button