Sports
Pogba Ya Jingine Bugawa Faransa Wasa Saboda Batancin Da Macron Ya Yi Wa Musulunci
Pogba Ya Jingine Bugawa Faransa Wasa Saboda Batancin Da Macron Ya Yi Wa Musulunci
Shahraren dan kwallo kafa na kasar Faransa mai bugawa kungiyar Manchester United ta kasar Birtaniya wasa, Paul Pogba, ya dakatar da bugawa kasarsa ta Faransa kwallo sakamakon batancin da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yi wa addinin musulunci.
A kwanakin baya ne shima dan wasan kasar Jamus me taka leda a kulob din Arsenal, Mesut Ozil aka dakatar da shi daga wasanni a Arsenal sannan aka dakatar da kwantiragin da yake wa kamfanoni da dama a sakamakon ya nuna fushinsa akan irin cin kashin da ake yi wa musulmai a kasashen duniya.