OZIL: Dan Kwallo Mai Kishin Addinin Islama Dake Fuskantar Kalubale Saboda Kishin Musulunci
Shahararren dan wasan kwallon kafa a duniya kuma dan kishin addinin musulunci Mas’ud Ozil na fuskantar kalubale saboda kishin musulunci da ya fito ya nuna a watannin baya.
A watannin baya ne Ozil ya fito ya caccaki duniya bisa shiru da ta yi alhali ana kashe musulmi ana cin zarafinsu bisa zalunci a sassan duniya ciki har da gabashin kasar Turkistan.
Bisa wannan kalami, makiya musulunci sun shiga sun fita domin su ga sun durkusar da shi, yanzu haka kungiyar da ya ke murzawa leda ta Arsenal ta ayyana cire shi daga jerin ‘yan wasan da za ta yi amfani da su a wannan shekarar.
Mas’ud Ozil haifaffen kasar Jamus kuma tsohon dan wasan kungiyar Real Madrid, kwararren dan wasa ne wanda ke da matukar hazaka a fagen tamaula, anyi amanna cewa yana daga tsirarrun ‘yan wasan da ke da matukar hadari da basira wajen samar da nasarar jefa kwallo a raga.
“Wannan sako ne mara dadi ga masoyana, hakika na yi matukar rashin jin dadi bisa rashin saka sunana a jerin ‘yan wasan da za su taka leda cikin wannan kaka, ina muku alkawari wannan mataki ba zai taba saka ni canza ra’ayina ba, zan cigaba da rayuwa wajen amfani da muryata na yaki danniya da zalunci ko ta halin kaka”
Inji Mas’ud Ozil.
Hakika musulunci da musulmi su na cikin babban kalubale a duniya, laifin wannan bawan Allah kawai shi ne don ya fito ya yi Allah wadai da zaluncin da ake wa musulmi sanda kasashen musulmi su ka yi shiru da bakinsu.
Idan za su iya dusashe tauraruwarsa a kallon kafa ba za su iya dusashe ta a duniyar musulunci da zukatan musulmi ba. Mas’ud Ozil zai cigaba da haskawa a zukatan musulman duniya.
Daga Indabawa Aliyu Imam