Na yi nadamar goyon bayan shugabanni marasa hankali Da kishin kasa – Fatima Ganduje Ajimobi
Fatima Ganduje -Ajimobi, diyar gwamnan jihar Kano, ta yi wallafa inda ta nuna damuwarta
Ta bayyana cewa, ta rasa me za ta ce amma tana matukar jin kunyar abinda tayi
Ta yi nadamar taba goyon bayan shugabanni marasa hankali da kuma rashin kishin kasa
Diyar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Fatima Ganduje Ajimobi, wacce ke auren dan marigayin tsohon sanata kuma gwamnan jihar Oyo, ta yi magana a kan shugabanni.
Fatima Ganduje Ajimobi ta ce ta rasa me za ta ce a wallafar da tayi amma tana matukar nadama.
Ta bayyana damuwarta tare da dana-saninta na goyon bayan shugabanni “marasa hankali kuma marasa kishin kasa.”
Kamar yadda ta wallafa, “Na rasa me zan ce kuma ina matukar jin kunya da na taba goyon bayan shugabanni marasa hankali da kuma kishin kasa.”
Fatima ta yi wannan wallafar ne bayan sa’o’i kadan da yin harbe-harbe ga masu zanga-zangar bukatar kawo karshen cin zarafin ‘yan sanda ke yi a Lekki tollgate da ke jihar legas.
Madogara: Legithausa.