Me Za’ayi Da Mai Goyon Bayan ‘Yancin ‘Yan Luwadi Da Madigo? (Hotuna) ~ Datti Assalafy
Karshen rashin wayewa da lalacewa da masifa da bala’i shine a wayi gari wani daga cikin mutane yana goyon bayan Luwadi da Madigo, dabi’ar da ko dabbobi basa yi
Duk wanda ya san bashi da data baya ganin hoto a Facebook kafin ya karanta wannan sakon to ya sayi data ya ga abinda yake kunshe a cikinsa, hakanan wanda baya fahimtar yaren turanci ya nuna ma wanda ya iya fassara ya fassara masa
Jama’a Aisha Yesufu a shekarar 2019 da farkon shekarar 2020 ta wallafa wasu sakonni a shafinta na Twitter kamar yadda zaku gani a screenshot tana bayyana cikakken goyon bayanta ga kungiyar ‘yan Luwadi da Madigo na duniya “Lesbian, Gay, Bisexual Transgender” (LGBT), ita a gareta suna da damar da za’a basu ‘yancin auren jinsi tunda basa tayar da hankali, bani da tabbacin ko ‘yar Madigo ce amma dai tana goyon bayansu a fakaice
An ruwaito Hadisi sahihi daga Manzon Allah (SAW) cewa idan ana Luwadi, Al’arshin Ubangiji yana girgiza saboda tsoron fushin Allah (SWT), sama tayi kamar zata fado a kan kasa, sai Mala’iku suyi riko da ita, su karanta Qulhuwallahu Ahad.. har karshen surar har sai sun samu nutsuwa daga fushin Allah Madaukakin Sarki akan masu Luwadi
Amma a gurin wannan mata Aisha Yesufu bayahudiya a rigar Musulunci ba laifi bane Luwadi da Madigo da auren jinsi, ‘yan Luwadi suna da damar da za’a basu ‘yanci
Tsakani da Allah Ya kamata a samu Musulmin kirki mai hankali da tunani da zai goyi bayan wannan matar ko ya ji yana sonta? Musulmi ka sani cewa tana samun dama da iko zata bada ‘yancin ayi Luwadi da Madigo tare da auren jinsi, wannan yana daga cikin dalilan da yasa yahudawa suke kambamata da kokarin daukaka darajarta
Ku dubi irin cin mutunci da ta yiwa ‘yan Arewa da Malaman addini a sakon bidiyo da ta fitar jiya don neman tunzura ‘yan Arewa, ku ji abinda ta fadi a kan shugaba Buhari wanda a haife yayi jika da ita, bata da kunya, fitsararriyace bayahudiya a rigar Musulunci, tana magana babu kunya tana gantsali sai kace wata tsohuwar kilaki
‘Yan uwa Musulmi ya kamata ku san hatsarin wannan matar, ku dena ganinta a matsayin wata jaruma, tana tattare da boyayyar manufa ga addinin Musulmi da kuma zaman lafiyar mu, gashinan ita da abokan huldarta ‘yan kwangila sun kunna wutar rikici wanda Allah ne Kadai Ya san yadda abin zai tsaya
A hukumance mun san ka’idar zanga-zanga wanda duk abinda ya faru na tashin hankali yana wuyan wadanda suka tsara zanga-zangar, don haka muna kira ga masu iko da tsaron Nigeria su tuhumi Aisha Yesufu da abokanta wadanda aka basu kwangilar shirya wannan masifa
Muna rokon Allah Ya wulakanta wannan mata
Allah Ka kaskantar da darajarta
Allah Ka daidaita al’amarinta
Allah Ka sa wannan masifar ya kare a kanta.
Ga hotunan nan kasa.