Kannywood

Matakin Da Arewa24 Na Dauka akan Bidiyon Tsiraicin Safarau

A yau shafin Hausaloaded ya samu labari daga marubucin nan mai suna Indabawa Aliyu Imam ya wallafa a shafin game da matakin da arewa 24tv sunka dauka akan fitar da vidon batsa na jaruma safarau ga jawabin nan nasa.
Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Malam Isma’il Na’abba Afakallahu ya tabbatar min da cire Safara’u kwana casa’in daga shirin na kwana casa’in, kuma na yi magana da wani tsohon ma’aikacin gidan inda shi ma ya tabbatar min da abinda Malam Afakallahu ya fa’da min.
Ita dai Safara’u ita ce jarumar shirin kwana casa’in da ta aikata bidiyon batsa wanda a wancan lokaci aka sami jama’a da dama da su ka yi Allah wadai da wannan jaruma kuma su ka bukaci gidan Arewa24 da ya gaggauta cire ta daga shirin na kwana casa’in wanda ni ma na kasance d’aya daga cikinsu.
Hakika Malam Afakallahu ya cancanci yabo bisa kokari da ya yi aka cire wannan yarinya aka maye gurbinta da wata, su ma Arewa24 sun yi abinda ya dace, dama tun a wancan lokaci Malam Afakallu ya ce min Arewa24 sun ce masa sun riga sun gama d’aukan shirin da ita zango na uku, shi ya sa ta kasance cikin shirin da suka saka.
Tabbas Arewa24 sun aikata abinda ya kamata, wannan zai zama darasi da izina ga sauran jarumai da su guji aikata makamancin abinda wannan yarinya Safara’u ta aikata, kuma hakan zai tsaftace shirin na su na kwana casa’in da ma tasharsu ta Arewa24 daga kazantar da wannan shaidaniyar yarinya ta aikata, dama tuni aka sami jama’a da dama da suka sha alwashin daina kallon shirin saboda ita.
Mu na fata Arewa24 za su cigaba da kar’bar korafe-korafe irin wannan bisa kusa-kuran da su ke aikatawa, ko mu kanmu da mu ke korafi ba wani abu ba ne ya sa mu hakan sai domin maslahar al’umma da maslahar tashar, burinmu su gyara kusa-kuran da su ke yi tasharsu ta zamanto tana amfanar da al’umma maimakon cutar da su, in dai za su gyara kusa-kuran da su ke yi mu ma babu abinda zai sa mu fito mu dinga caccakarsu.
A karshe muna tunatarwa ga Hukumar Hisbah ta jahar Kano bisa alkawari da su ka d’auka na gurfanar da wannan yarinya a gaban kotu, ina tuna yadda DG na Hukumar hisba ta Kano Dr. Aliyu Kibiya ya sha alwashi cewa hukumarsu ta hisba ba za ta kyale wannan yarinya haka nan ba dole za su d’auki matakin da zai zamo jan kunne gare ta da kuma darasi ga ‘yan baya, duk da ya ke a wancan lokaci hukumar ta bada uzuri da matsalar annobar Korona, yanzu Alhamdullillah Allah ya sawwaka mana wannan Annoba mun zuba ido mu ga abinda hukuma za ta yi, shin za ta d’auki matakin da ta sha alwashin d’auka wanda dama asali gwamnati ta samar da ita domin ire-iren hakan, ko kuwa za’a bar abun ya tafi haka nan.
A karshe muna yabawa Kwamandan wannan hukuma Sheikh Haruna Muhammad Ibn Sina bisa jajircewa da aka bamu labari ya na da ita, zan kuma yabi Ustaz Imam Mhd Mikail Albakry kwamushinan Hukumar zakka da hubusi na biyu, a wancan lokaci da abun ya faru ya na hukumar hisba, kuma har ga Allah yayi kokari ya jajirce wajen ganin an d’auki mataki akan wannan yarinya tun a farkon lamarin, Allah ya saka masa da alkhairi ya kuma baiwa hukuma ikon d’aukar mataki.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button