Mansurah Isah Ta Bayyana Dalilin da yasa Bata Taba cewa Ita cikakkiyar ‘yar Arewa bace
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa,Mansurah Isah ya nuna Alhini kan abinya faru akan zanga-zangar SARS a fadin Najeriya.
Ta bayyana ta shafinta na sada zumunta cewa jiya ta sha kuka sosai.
Wata ta tambayeta ya maganar zanga-zangar da ta shirya yi ranar Alhamis?
Mansurah ta bayyana cewa ta dakatar da ita dan ba zata so a dalilinta wani ya rasa ransa ba.
Wani ya bayyanawa Mansurah Cewa ne zai hana ta koma kudu dan abinda take magana akai tanawa kudu ne ba Arewa ba. Ya zargi Mansurah da cewa bata taba magana akan satar mutane da kuma kisa da ake yi a Arewa ba.
Saidai mansurah ta gaya masa cewa kai mahaukacine, amma bana zarginka, sun riga sun canja tunaninku akan karya. Kai zaka rantse da Allah ban taba magana akan ci gaban Arewa ba? Wannan dalili yasa ban taba cewa ni cikakkiyar ‘yar Arewa bace, saboda sakarkarun mutane shegu irinka, wanda basu da hankali kuma basu samu tarbiyya ba.
Nil
I am civil servant