Labarai

Mahaifi Ya Kashe Ɗiyarsa Ƴar Watanni 9 Ta Hanyar Yi Mata Fyaɗe

 
Hukumomi a ƙasar Amurka sun kama wani mahaifi, Austin Stevens ɗan shekaru 29 da ake zargi da yiwa ƴarsa ƴar watanni 9 fyade.
An kama mutumin ne bayan da ya kira lambar karta kwana ta 911 inda yayi ƙorafi akan yanayin ɗiyar tasa, Zara Scruggs wadda ba ta daɗe da fara koyon tafiya ba.
Ƴan sandan Montgomery dake Pennsylvania sun bayyana cewa an ga fanfas ɗin yarinyar cike da jini, sannan al’aurarta da duburarta sun lalace. Sun kuma bayyana cewa cikin gaggawa bayan samunta a wannan hali aka garzaya da ita Asibiti inda ƙasa da awanni 2, likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Majiyarmu ta samu ne daga shafin dokin karfe  cewa,mahaifin yarinyar ya amsota ne daga hannun mahaifiyarta wadda suka daɗe da rabuwa da niyyar ta kwana a hannunsa kamin daga baya ya mata wannan aika-aika.
An kamashi, sai dai kotu ta bayar da belinsa akan Dala Miliyan 1 kamin a kammala bincike, duk da dai har yanzu babu wanda ya karɓi belin nasa.
An fara tarawa mahaifiyar yarinyar, Erica Scruggs kudin tallafi wanda zuwa yanzu sun kai Dala Dubu 28. Ranar 13 ga watan October ne ake sa ran fara sauraren ƙarar.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button