Labarai

Kace Najeriya na sayar da Mai arha fiye da kasar Saudiyya amma kasan cewa a kasar Saudiyya mafi karancin Albashi Naira Dubu Dari 3 ne?~ Bulama Bukarti ga Buhari

A yayin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi magana akan saukin farashin man Fetur a Najeriya idan aka kwatantashi da na sauran kasashe, musamman kasar Saudiyya wadda itace ta daya wajan fitar da man A Duniya, ‘yan Najeriya sun fara mayar da martani.
 
Bulama Bukarti wanda sanannen Lauya ne me ikirarin karw hakkin bil’adama da kuma kokatin tsage gaskiya ya bayyana cewa, shugaba Buhari yace Saudiyyar na sayar da man Fetur da tsada fiye da Najeriya amma kuma ya sani mafi karancin Albashi a Saudiyya kwatankwacin Naira 305,000 ne wanda ya kama Riyal 3,000.
Ya kara da cewa ka biyamu irin wancan Albashin, muma zamu biya Naira 168 a matsayin kudi  man fetur na kowace lita, kamar kasar Saudiyya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button