Labarai
Ka lura, Masu zanga-zanga ba SARS ne basu so ba kai ne basu so~ Marafa ya gayawa Buhari
Advertisment
Yace sai gwamnati ta lura kada ta fada tarkon Makiya. Akwai wanda zasu iya yin komai dan kawar da ita. Yace amincewa da dakatar da SARS ka iya jefamu cikin matsalar da ta fi wadda muke ciki, musamman daga bangaren da ya fito(jihar Zamfara). Yace wadannan mutanen ne dai nan gaba zasu iya fitowa kuma su soki gwamnati kan cewa ta kasa kare rayuwar ‘yan kasa.
Hutudole na ruwaito,Marafa ya ci gaba da gayawa Dailytrust cewa, Wannan zanga-zanga ba akan SARS bane akan gwamnati me ci ne. Wasu da basa farin ciki da wannan gwamnatin na so su tayar da fitina. Yace kamin a ankara zakaga matsalar ta karade kasar, ta yaya zamu rayu ba tare da SARS ba? Abune me wuya.