Labarai

Jami’an Tsaro kusan Dubu 34 Ne aka kai su kula Da zaben Ondo

 
A gobe, Asabar, 10/10/2020 ne idan Allah ya kaimu za’a yi zaben gwamnan jihar Ondo inda za’a kara tsakanin manyan ‘yan takara 3, Gwamna me ci na jam’iyyar APC,  Rotimi Akeredolu,  da mataimakinsa na jam’iyyar ZLP, Agbola Ajayi da kuma dan takarar PDP, Eyitayo Jegede.
 
Zuwa yanzu dai alamu sun nuna cewa hukumar zabe me zaman kanta, INEC tawa zaben shiri me kyau inda tuni aka fara tafiya da kayan zaben zuwa kananan hukumomi.

Wasu masu saka ido a kan harkar zaben da gidan talabijin din TVC ya zanga dasu a wani shiri da wakilin hutudole ya bibiya sun bayyana gamsuwa da shirin da INEC tawa zaben na Ondo.
 
shafin Hutudole ne na ruwaito,jami’an tsaro sun nuna gwanji da kuma baiwa jama’ar jihar tabbacin cewa zasu bada tsaro a lokacin zaben inda suka zagaya cikin birnin jihar, Akure da jiniya.
 
Rahoton yace jami’an tsaron da suka hada dana Sojoji, ‘yansanda, Civil Defence,  Road Safety sun kai kusan Dubu 34.

Saidai rahoton yace wannan zagaye da jami’an tsaron suka yi be firgita jama’ar jihar ba inda wasu yara ma wakoki suka rikawa jami’an tsaron suna jinjina musu, hakanan wasu masu kada kuri’u sun jaddada cewa zasu fita su dangwala kuri’arsu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button