Labarai

INEC ta sanar da ranar zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya

INEC ta sanar da ranar zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta sanar da ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.
Wani babban jami’in hukumar Nick Dazang, ya tabbatar wa BBC da cewa Shugaban na INEC Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.
Ya kuma jaddada cewa tuni hukumar ta tsayar da mako na biyu na kowace Fabrairun shekarar zaɓe a matsayin makon da za a rinƙa gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.
Sai dai har yanzu hukumar ba ta sanar da ranar da aka tsayar ba doimin gudanar da zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisa ba a ƙasar.
A shekarar 2019 dai, an saka ranar 16 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaɓen shugaban ƙasar, amma saboda wasu dalilai aka ɗaga ranar zaɓen zuwa 23 ga watan Fabrairun.
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button