Labarai

Ina Godiya Ga ‘Yan Nijeriya Bisa Haƙurin Da Suke Yi ~ Cewar Shugaba Buhari

 
Shugaban kasa ya bayyana gaban yan majalisar dokokin tarayya domin gabatar da kasafin kudin 2021 a ranar alhamis
Shugaba Muhammad Buhari ya jaddada niyyar gwamnatinsa na inganta rayuwan yan Najeriya gaba daya. Ya godewa shugabannin majalisan dokokin tarayya bisa hadin kan da suke bashi da gwamnatinsa
Shugaba Muhammadu ya fara jawabinsa na gabatar da kasafin kudin 2021 da mika godiya ga yan Najeriya bisa hakuri, jajircewa da goyon bayan da suka cigaba da nunawa gwamnatinsa duk da halin kuncin da ake ciki.
Buhari ya bayyana cewa gwamnatin ta samu nasarori daban-daban a kasafin kudin 2020.
Shugaban kasan ya tunawa yan majalisan cewa an yi wasu sauye-sauye cikin kasafin kudin 2020 sakamakon bullar cutar Korona domin takaita illar da za ta yiwa tattalin arzikin kasar.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta cigaba da kokarinta wajen samar da rana gobe mai kyau ga Najeriya.
Yace Mun godewa dukkan yan Najeriya bisa hakurinsu da cigaba da nuna mana goyon baya cikin wannan lokaci mai wuya. Zamu cigaba da kokarin cika manufarmu da samawa Najeriya rana gobe mai kyau.
Shafin rariya ne sunka ruwaito wannan labari.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button