Labarai

IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya

Sanarwar na zuwa ne bayan al’umma sun shafe kwanaki suna zanga-zanga a tituna da kuma dandalin sada zumunta na neman a soke rundunar a kasar baki daya don kisa da cin zarafin al’ummma da suke yi.

Yayin jawabin, IGP ya ce, “An soke Rundunar tarayya ta musamman masu yaki da fashi da makami da aka fi sani da SARS a dukkan rundunonin ‘yan sanda da ke jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.”

 
Bayan jawabin, kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa DCP Frank Mba ya fitar da wata sanarwa mai taken, ‘IGP ya soke rundunar ta musamman mai yaki da fashi da aka fi sani da (SARS)’, wani sashi na cikin sanarwar ya ce:

Bisa la’akari da kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya suka yi, za a tura jami’an tsohuwar rundunar ta SARS da aka rushe zuwa wasu sassa karkashin rundunar ‘yan sandan nan take.

“IGP din ya ce ta  rundunar ta san cewa akwai bukatar ayi yaki da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka da ke karuwa a kasar da a baya rundunar ta SARS ke yi.”

Majiyarmu ta  fara samun wannan rahoto daga shafin Legit hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button