Labarai

Gwamnatin Nijeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Tallafin Bashin Kudade Masu Yawa Domin A Bunkasa Musu Harkokin Kasuwancinsu

Gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammad Buhari, ta bude shafin baiwa matasa tallafin bashin kudade masu yawa domin a bunkasa musu harkokin kasuwancinsu, a karkashin ma’aikatar matasa.

Babban Bankin Nijeriya wato CBN tare da hadin guiwar bankin NIRSAl MICROFINANCE BANK, suka dauki nauyin tattara bayanai masu bukatan bashin tallafin da gwamnatin kasar zata bayar.

Kowa ya shiga wannan link din domin ya nemi bashin

https://nyif.nmfb.com.ng/

Yana da matukar saukin cikawa, amma matasa kadai za’a baiwa bashin, kowa ya tabbata ya saka lambar BVN dinshi daidai, kuma sunan da zaka saka ka tabbata shine a jikin BVN din naka, dole sai ka cika wannan sharadin kafun su baka damar neman bashin.

Ina yiwa kowa fatan Alkhairi, Allah yasa al’ummar yankinmu na Arewa su amfana.

Karkashin wallafar rariya ne inda Hausaloaded nayi bincike inda tabbas akwai wannan tsari.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button