Labarai

Gwamna Babagana zulum Ya Fadi wani Sirin Yakar Boko Haram

 
Mai Girma Gwamnan Babagana Zulum ya shawarci sojoji su rika bin ƴan ta’adda zuwa maɓoyansu ba su rika jira sai sun kawo hari ba
– Zulum ya kuma ce akwai bukatar sojojin su rika gina alaƙa mai kyau da mutanen gari ta yadda za su rika taimaka musu da bayyanan sirri –
Voice of borno sune na ruwaito cewa kazalika, ya shawarci a rika nada sojojin da suka dace wurin jagorancin rundunar da ke yaƙi da ƴan ta’adda Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya lissafa wasu hanyoyi da ya yi imanin idan sojoji sun bi za su iya cin galaba kan Boko Haram. Gwamnan ya yi wannan jawabin ne wurin taron hadin gwiwa na shugaban sojojin ƙasa na shekarar 2020 da aka yi a Maiduguri a jihar Borno inda shine babban baƙo na musamman. Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram –
A cewarsa rundunar sojojin za ta yi nasara ne kan ƴan ta’addan na Boko Haram idan ta sauya dabarun yaƙin ta. Ya jijinawa ƙoƙarin sojojin amma duk haka ya ce yana da kyau “mu fada wa juna gaskiya lokutan da muka lura abubuwa suna taɓarɓarewa.” Ya ce gwamnatinsa ba za ta gajiya ba wurin taimakawa sojojin da abinda suke buƙata. A cikin jawabinsa ya bayyana cewa ya kamata sojojin su rika bin ƴan ta’addan zuwa maɓuyansu suna halaka su ba wai su rika jira sai an kawo musu hari sannan su kare ba. “Ku dena jira kuna bawa ƴan ta’addan daman su fara kawo harin farko. Tsarin ku ya zama bibiyan duk wasu ƴan ta’addan da suka yi saura bayan kun kai hari.”
Ƴa kara da cewa ya kamata sojojin su gina alaƙa mai kyau da al’ummar yankin. “Ya zama dole rundunar soji ta gina alaƙa mai kyau da al’ummar garuruwan da suke aiki ta yadda za su rika taimaka musu wurin tona ƴan ta’addan da ke tsakaninsu da masu taimaka musu,” in ji shi.
Gwamna Zulum ya kuma yi kira ga Shugaban Sojojin ya duba batun naɗa sojojin da suka Ƙware a matsayin kwamandojin ƴaki da ƴan ta’adda. Gwamnan ya kuma yi alhinin mutuwar Kwanel Dahiru Baƙo wadda ya mutu makonni da suka gabata yayin wani hari da Boko Haram suka kai.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button