#EndSARS: Atiku ya gargaɗi Buhari kan amfani da ƙarfin jami’an tsaro akan masu zanga zanga
#EndSARS: Atiku ya gargaɗi Buhari kan amfani da ƙarfin jami’an tsaro akan masu zanga zanga
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana baƙin cikinsa game da yadda ƴan daba suka afkawa masu zanga-zangar lumana ta #EndSARS wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka.
Tsohon ɗan takaran shugaban ƙasa a jam’iyar PDP a 2019 ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Facebook a yammacin yau Talata.
Wazirin Adamawa, ya ce masu zanga zangar nan ba haka kawai suka fito ba sannan basu saba doka ba, hasalima inda gwamnati ta biya musu buƙatunsu da ba a kai ga inda ake a yanzu ba. D haka ne ya gargaɗi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga amfani da ƙarfin jami’an tsaro akan masu zanga zangar.
“Ina ƙira ga gwamnatin Buhari kada ta kuskura ta yi amfani karfi kan masu zanga-zangar #EndSARS”
Atiku Abubakar ya buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da yayi gaggawar aiwatar da buƙatun masu zanga-zangar tare da ƙira a gashe daga ƙarshe da ya fito ya yi wa al’ummar Najeriya jawabi da zai kwantar da hankali musamman ga matasa.