Addini

Daga Fara Ƙaryata Hadisai har ya Isa ga Kafirci ~ Sheikh Aliyu Muhd Sani

A daidai lokacin da Shugaban Ƙasar Faransa yake cewa za su cigaba da zana hotunan ɓatanci (cartoon) ga Annabi Muhammad (saw), a lokacin ne kuma shugaban masu sukar Sahihul Bukhari da Muslim na wannan zamani ya bayyana cewa, -wai- ba dole sai mutum ya yi imani da Annabi Muhammad (saw) kafin ya shiga Aljanna ba.
Shi wannan Ɗan Boko Aƙida ɗan Ƙasar Misra, mai suna Islam Behery, shi aka kama ya fara ƙaryata auren Nana A’isha (ra) tana ƴar shekara tara (9), sai ga shi yau ya isa inda ya nufa, wato ƙaryata Manzancin Annabi Muhammad (saw), da mai da shi akwai da babu duk ɗaya.
Wannan abin da ya faɗa kafirci ne ta kowace fiska, ya warware tushen Addinin Muslunci, ya ƙaryata Allah, inda ya ce:
{وَمَنْ لَمْ يُؤْمِنْ بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ فَإِنَّا أَعْتَدْنَا لِلْكَافِرِينَ سَعِيرًا} [الفتح: 13]
“Duk wanda bai yi imani da Allah da Manzonsa ba to lallai mun tanadar wa kafirai wutar Sa’ira”.
Ma’ana; wanda bai yi imani da Allah da Manzonsa ba kafiri ne, ɗan wuta, ba zai shiga Aljanna ba.
To haka dai a kullum ake yaƙar Muslunci ta cikin gida da ta waje, da sunan ƴancin faɗin albarkacin baki, ko da sunan tace Hadisan Annabi (saw). Daga maganar tace Hadisai ya isa zuwa ga halasta kafirce ma wanda ya faɗi Hadisan.
Saboda haka wannan shi ne halin da ake ciki. Ƴan Boko Aƙida da Ƴan Bidi’a suna yaƙar Addini ta cikin gida, su kuma kafirai suna yaƙarsa ta waje, kuma suna samun ɗaurin gindinsu. Wannan ya sa suke sukar wanda ya kashe Malamin Makaranta a Faransa, amma suka manta da shi Malamin Makarantar da ya ci zarafin Annabi Muhammad (saw).
A taƙaice saƙon da nake son isarwa shi ne; an kama mai sukar Hadisan Sahihul Bukhari da Muslim, mai ƙaryata auren Nana A’isha (ra) tana ƴar shekara tara (9), an kama shi yana ƙaryata Manzancin Annabi (saw), yana cewa; ba dole sai an yi imani da Annabi Muhammad (saw) ba kafin a shiga Aljanna. Ma’ana dai, yana so ya ba da lasisin shiga Aljanna ga iyayen gidansa Yahudawa da Nasara.
Saboda haka kun ga yadda ƙaryata Hadisan Annabi (saw) yake kaiwa ga Kafirci da warware ginshiƙan Muslunci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button