Labarai
Da Dumi-Dumi: Sabuwar Rundunar SWAT ce zata maye SARS
Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya bayyana sabuwar Rundunar Special Weapons and Tactical Team, SWAT a matsayin wadda zata maye Rundunar ‘yansanda ta SARS.
Sanarwar ta bayyana cewa ‘yansandan da zasu yi aiki a wannan sabuwar Runduna za’a musu gwajin lafiya da kuma na kwakwalwa dan tabbatar da cewa basu da matasala.
A mako me zuwa ne idan Allah ya kaimu za’a farawa ‘yansandan da zasu yi aiki a wannan Runduna horo.
Da ya ke yan kudu su ne mutane shi ya sa a ka magance matsalarsu cikin sauri,amma ta mu matsalar ta ki ci ta ki cinyewa har yau ba adaina kashe kashe ba da garkuwa da mutane.