Labarai

Buhari ya ce soke SARS matakin farko ne na sauya fasalin aikin ƴan sanda a Najeriya

A karon farko shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fito ya yi wa ƴan ƙasa jawabi kan soke rundunar ƴan sanda ta Sars.

Shugaba Buhari ya ce soke rundunar matakin farko ne a sauye-sauye masu tsauri da zai aiwatar kan aikin ƴan sanda domin tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi aikin da ya dace da kare rayuka da dukiyoyi.

Buhari ya ce gwamnati ta damu da ƙorafin ƴan Najeriya kan amfani da ƙarfi sama da kima da ƴan sanda ke yi a wasu lokutan da kuma kisa mara dalili.

Jawabin shugaban na minti ɗaya da rabi a shafin Twitter ya ce gwamnati za ta tabbatar duk wadanda ake zargi ko da hannu a cin zarafi su fuskanci shari’a.

Sannan ya nuna takacinsa kan mutuwar mutum guda a jihar Oyo a yayin zanga-zangar #EndSars, kuma ya umarci a gudanar da bincike kan musababin mutuwarsa.

Shugaban ya ce aikin ɗan sanda shi ne kare ƴan ƙasa don haka ba za a lamunci wasu kalilan ko ɓata gari su kasara kimar aikin jami’an tsaro a Najeriya ba.bbchausa ne ta ruwaito.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button