Labarai

Buhari ya ƙara wa malaman makaranta albashi

 
Shugaba Muammadu Buhari na Najeriya ya amince da ƙarin albashi ga malaman makaranta a faɗin ƙasar.
Kazalika, ya ƙara yawan shekarun ritaya ga malaman daga 35 zuwa 40.
Buhari ya bayyana hakan ne ta bakin Ministan Ilimi Adamu Adamu, wanda ya wakilce shi yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya ranar Litinin a Abuja.
jaridar bbchausa na ruwaito,Buhari ya ce an ɓullo da sabon tsarin albashin ne domin ƙarfafa gwiwar malaman wurin zage damtse a aikinsu.
Ya zuwa yanzu fadar shugaban ba ta bayar da cikakken bayani ba game da yadda za a aiwatar da sabon tsarin.
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button