Addini

Bidiyo: Sheikh Abdallah Ya Fadi Wani Sirrin Gwamna Zulum Mai Matukar Ban Mamaki



Cikin bidiyo Sheikh Dr Abdallah Usman Gadon-kaya yayi bayanin cewa Allah bai taba nuna mana wani gwamna  a Nigeria wanda ya kai Gwamna Zulum ba, domin alkhairansa da mutuncinsa da tsoron Allahnsa ya bayyana

Malam yaci gaba da cewa, wani makusancin gwamna Zulum ya fada masa cewa, tunda yake tare da Zulum ya sanshi bai taba fashin Azumin ranar Litinin da Alhamis ba saboda neman kusancinsa da Allah

Malam yace, an fada masa a duk lokacin da Gwamna Zulum ya fita zuwa wani gari Boko Haram suka tare hanya, idan suna harbi fitowa yakeyi daga mota ya tunkari ‘yan Boko Haram din yana kuka yana zubar da hawaye, sai jami’an tsaro ne zasu rikeshi su ja shi jikin mota mai sulke yana kuka, yana cewa ku barni shahada nake nema

Hakika nima gwamna Zulum yana bani mamaki, kuma hakane, bai yiwuwa a samu Musulmi da irin wannan nagarta nasa da rashin tsoro ba tare da an sameshi ma’abocin addini da ibada ba

Daga karshe Dr Abdallah yayi kira garemu talakawa Nigeria da cewa mu hadu mu tsayar da Zulum takaran shugaban kasa idan Allah Ya kaimi 2023

Yaa Allah Ka daukaka darajar Gwamna Zulum Ka kareshi, Allah Ka kaishi matsayin shugaban kasar Nigeria Amin

Ga bidiyon nan sai ku saurara daga bakin Sheikh Abdallah









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button