Babban Kuskuren Da Dan Arewa Zai Yi Idan Allah Ya Kai Mu 2023 Shine Ya Goyi Bayan Bola Ahmad Tinubu! Daga Imam Murtadha Gusau
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku jama’ah! A daidai wannan lokaci da yankin mu na arewacin Najeriya mai albarka yake cikin halin ni-‘ya-su, yake cikin halin damuwa, musamman bangaren rashin tsaro, talauci, rashin ababen more rayuwa, da sauran su. A lokacin da yankin yake bukatar kulawar shuwagabanni, tun daga zamanin tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Ebele Jonathan har zuwa yau, wallahi ba mu taba yin babban kuskuren da ya kai mu zabi jigon jam’iyyah mai mulki ta APC, kuma tsohon gwamnan Jihar Legas, wato Bola Ahmad Tuninbu ba!
Wallahi duk wanda yake bibiyar siyasar kasar nan, daga shekarar 1999 zuwa yau, ya san irin ta’asa da ta’annati da Tinubu yayi wa al’ummar arewacin Najeriya. Kuma babu wani wanda ya isa ya fada muna cewa Tinubu yana son arewa da ‘yan arewa, har mu saurare shi.
Jama’ah, mu tuna fa, su Tinubu ne suka kirkiri wata jama’ah mai suna OPC, a lokacin da yake gwamnan Jihar Legas. Wadannan mutane, wato OPC, duk shekara sai sun kashe ‘yan arewa mazauna Legas. Sun ware ranar June-12 na kowacce shekara domin kisan gilla ga ‘yan arewa mazauna Legas.
Sannan Tinubu yana cikin wadanda suka hana shugaba Muhammadu Buhari ya bude iyakokin arewa, domin su samu saukin rayuwa. Shine ya tsaya tsayin daka domin ganin cewa sai dai a bude iyakokin Legas kawai. Nufin sa anan shine, duk harajin da ake shigowa da kaya ya kasance sune kawai za su ci gajiyar abun, ban da arewa.
A takaice dai, ina mai shaida maku cewa, wallahi, goyon bayan Tinubu a 2023, yana nuna rashin kishin arewa, ko kuma rashin sanin ciwon kai, ga duk wanda yayi kuskuren yin hakan. Don haka wallahi, sai muyi hattara!
Sannan duk mutumin da yake raye a kasar nan, kuma yake bibiyar al’amurran gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, yana sane da cewa, mutanen nan, wato su Tinubu, sun amfana matuka da gwamnati mai ci, ko kuma in ce wallahi sun fi kowa amfana, amma don rashin godiyar Allah, ku kalli yadda suka koma can karkashin kasa, suna yiwa gwamnatin bita-da-kulli, suna yi mata zagon-kasa. Suka koma can a boye, suna zuga ‘yan iska da zauna gari banza, matasa marasa aikin yi, da shugabannin coci-coci, wadanda suka mayar da addini abun wasa, wadanda yawancin su ‘yan kudu ne, makiya yankin arewa, suka koma suna yiwa wannan gwamnati tawaye da zanga-zanga. Wallahi ko dan jahila yasan da cewa wasu hamshakai ne suke daukar nauyin wannan zanga-zanga ta END SARS, kuma ba komai yasa suke wannan ba sai don su tozarta gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, kuma su tozarta arewa da ‘yan arewa, wannan shine kawai manufar su. Kuma duk suna yi ne domin maganar siyasar 2023, wato dole idan Buhari ya gama ya mika masu mulki da-karfi-da-yaji.
Saboda haka wallahi, ina kira ga ‘yan arewa da mu farka, mu san irin kulle-kulle, da makircin da ake kulla muna!
Ni fa ba wai ina nufin cewa babu kura-kurai a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bane, a’a, amma abunda nike kokarin nuna muna shine, makiyan arewa da ‘yan arewa sun sa yankin a gaba, suna amfani da zaluncin da wasu jami’an ‘yan sandan SARS suke yi, domin su durkusar da arewar baki daya.
Duk amfanar da su Tinubu suke yi da wannan gwamnati, amma basu gode ba, sun zama butulu, sai sun koma can karkashin kasa, suna yiwa arewa zagon-kasa, da kulla mata makirci.
A yau din nan Allah ya tona asirin su. Wani Farfesa, masanin tarihi da harkokin kasashen waje, malami a jami’ar Ibadan, mai suna Farfesa Alexander Adebisi, ya fito ya bayyana wa duniya cewa, suna da cikakkun hujjojin da ke nuna cewa su Tinubu ne suke daukar nauyin wannan zanga-zangar ta END SARS, domin ya fara fahimtar cewa kamar jiga-jigan siyasar arewa ba zasu goyi bayan takarar sa ba. To shine yake daukar nauyin ‘yan iska, domin a bata arewa da ‘yan arewar! Kuma ance yadda ya samu sa’ar matasan kudu, haka ma yana nan yana kokarin samun sa’ar matasan arewa don su ma su shiga wannan zanga-zanga. Don haka wallahi ‘yan uwana, ‘yan arewa, sai muyi hattara. Wallahi bamu da wani wurin da ya kai arewa!
Kuma duk mai hankali zai yarda da wannan Farfesan, domin irin makudan kudade da ake kashewa wurin gudanar da wannan zanga-zanga, wallahi sun wuce hankali, kuma sun wuce tunanin duk wani mai tunani. Irin abincin da ake ci da abun sha da sauran su, zai sa mu kara yarda da cewa, wannan abu yafi karfin yara, matasa, a’a, wasu manya ne, marasa kishin Najeriya, suke daukar nauyin wannan iskancin, kuma ba don komai ba, sai domin su cimma burin su na siyasa. Don haka yanzu ya rage namu. Shin zamu bari ayi amfani da mu? Shin zamu bari wasu ‘yan iska su lalata muna yanki, saboda biyan bukatar su?
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.