Ba ni da hannu a shirya zanga-zangar #EndSARS – Tinubu
Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nisanta kansa daga zanga-zangar EndSARS da matasa suka shafe mako biyu suna yi a wasu jihohin ƙasar.
Mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, ya faɗa cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar cewa ba daidai ba ne a ce mai gidan nasa ne ke ɗaukar nauyin zanga-zangar, kamar yadda ake yaɗawa.
Ya ce abu ne mai wuya Tinubu ya iya ɗaukar nauyin zanga-zangar a duka jihohin da ake yi.
“Ba zai yiwu Asiwaju Tinubu ya ɗauki nauyin zanga-zangar da ta toshe ɗaya daga cikin hanyoyin shiga da fita daga Jihar Legas ba, wadda take ɗaya daga hanyoyin samun kuɗin shiga ga gwamnatin jihar,” a cewar sanarwar.
“Kazalika, ba zai yiwu ya ɗauki nauyin zanga-zangar ba a jihohin da su kansu masu zanga-zangar ke adawa da shi.”
Haka nan sanarwar ta ce Tinubu ya aminta cewa ya kamata a rushe rundunar SARS sakamakon “lokaci mai tsawo da ta ɗauka tana cin zarafin matasa da sauran ‘yan ƙasa” kamar yadda masu zanga-zangar suka buƙata.
Sai dai ya ce ya kamata a nemi hanyoyin lumana domin gabatar da buƙatu ga gwamnati.
Mako biyu kenan ana zanga-zangar neman rushe rundunar ‘yan sanda ta SARS a Najeriya, sai dai zarce zuwa ta neman sauya salon mulki bayan Gwamnatin Tarayya ta rushe tare da maye gurbin SARS ɗin da SWAT.
Rahoto: bbchausa