Audio : Network Marketing Haramun Ne ~ Dr. Engr. Bashir Aliyu Umar
Audio : Network Marketing Haramun Ne ~ Dr. Engr. Bashir Aliyu Umar
Lallai dama duk wani platform, ko wani tsari ko kuma ma wata manhaja da za’a zo da ita ace kayi rajista, sannan ya kasance a baka wani bonus haka nan, sannan daga bisani a gindaya maka sharadin cewa ba zaka iya cire wannan bonus da aka baka ba har sai kayi referring mutane kaza sun sanya wani adadi na kudi sannan a baka damar cirewa, to aiko ya kamata ka fahimci cewa kawai ponzi scheme ne kuma kudinku da suke amsa sune suke cire wani abu su biya yan gabanku da su.
Idan kun lura mafi yawancin ponzi schemes suna fakewa da cewar suna running wani business wanda da ribar da suke samu ne suke baku. A wasu lokutan har business na bogi ma sukan iya nuna muku don dai kawai su saye tunanin ta yadda zaku gamsu da su kuga kamar da gaske suke. Amma inda kuka sanya kaifin basira a lokacin zaku fahimci cewa karya ce suke yi, yan damfara ne kawai.
Daga 2010 zuwa yanzu kadai anyi ponzi schemes da bazan iya kawo iyakar adadinsu ba ta siga daban-daban wanda dukkaninsu daga karshe durkushewa sukabyi saboda dama ba gaskiya aka shirya a cikinsu ba karyace da yaudara gami da tsagwaron damfara da ake yima wasu shigo-shigo ba zurfi su rufta.
Allah ya kiyaye….
Domin sauraron karin bayyani daga Dr Engr Bashir Aliyu Umar ga link nan kasa.