Kannywood
An kashe Dan Uwan Jarumi Yakubu Muhammad A Bauchi
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un
Tauraron fina-finan Hausa, Yakubu Muhammad ya bayyana cewa an kashe dan uwansa a wani kaute dake jihar Bauchi.
Yace lamarin ya farune da safiyar yau. Yakunu ya sanar da rasuwar dan uwan nasane a shafinsa na Instagram inda ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen sun tafi.
Shi kuma dan uwansa dama san kasuwa ne ya je siyan shinkafa a kauyen yayin da mutanen kauyen sun fito daukar fansa, yace a hakane aka rutsa da dan uwan nasa mutanen kauyen suka kasheshi.