Jarumi Ibrahim Maishinku Yayiwa Buhari Addu’a Mai zafi
Jarumi Ibrahim Maishinku Yayiwa Buhari Addu’a Mai zafi
A yau ne jarumi Ibrahim Maishinku Yayiwa Buhari Addu’a mai daukar hankali akan yana da kyau duk wani dan Najeriya musulmi ya dukufa wajen yiwa shugabansa.
Yayi wannan addu’a a ne a shafinsa na Instagram.
“Ya Allah ga bawan nan dai naka da Ka ara wa mulki a lokacin da basu so ba,
Ya Allah ka tserar da shi a lokacin da suka nemi hallaka shi da harin bomb
Ya Allah ka warkar da shi a lokacin da suka shayar da shi guba,
Ya Allah muna da yaqinin yanzun ma ba zaka barshi ba,
Ya Allah muna tawassuli da sunayen ka tsarkaka,
Ya Allah muna tawassuli da mafi adalcin shugaba, masoyin ka, annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam,
Ya Allah muna tawassuli da kyawawan ayyukan mu,
Ya Allah Ka yi riko da hannunsa,
Ya Allah Ka shiga cikin lamuransa
Ya Allah ka kare shi daga sharin makiya kasar mu,
Ya Allah Ka yafe mana
Ya Allah Ka bamu lafiya da zama lafiya,
Ya Hayyu Ya Qayyum
Ya zul jalali Wal Ikram.”
gaskiya ne mai shunku allah saka da wanga addu’a