Labarai
Shigar Nuna Tsiraici : Fatima Nuhu Ribaɗo Amarya Dan Atiku Abubakar ta yi martani
Advertisment
Shigar Nuna Tsiraici : Fatima Nuhu Ribaɗo Amarya Dan Atiku Abubakar ta yi martani
Ƴar tsohon Shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribaɗo ta yi martani kan hotunan ta da aka fitar a ranar aurenta wanda ya janyo cecekuce.
Fatima wadda ta auri ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar wato Aliyu Atiku Abubakar (Turakin Adamawa) ta nuna nadamar ta kan bayyana hotunan duk da ta bayyana cewa a cikin gidansu aka ɗauki hototunan dake bayyana jikinta kuma aka baza a duniya.
Ta yi alƙawari da cewa hakan zai zame mata darasi domin gyara wannan kuskure da ta yi a gaba.
Daga ƙarshe ta miƙa godiya ga ƙawaye da ƴanuwanta har ma da wadanda suka yi mata fatan alkhairi.