Labarai

Za’a Fuskanci Ƙarancin Man Fetur ~Datti Assalafy

Advertisment

Daga gobe talata kungiyar direbobin Nigeria masu dakon man fetur zasu dunguma yajin aikin da babu ranar dawowa, saboda gwamnatin Nigeria ta rage musu adadin litar man fetur da zasu dinga dauka

Direbobin sun rena adadin da gwamnatin Nigeria ta gindaya musu, sun nemi da a kara amma gwamnatin taki, wannan ne dalilin da yasa zasu tsunduma yajin aiki sai babba ta gani daga gobe talata

Ita kuma gwamnati tayi hakane domin ta inganta lafiyar titunan kasa sakamakon manyan motoci da suke bi suna lalatawa saboda kaya mai nauyi da suke dauka

Don haka ‘yan Nigeria suna fuskantar mummunan barazana na karanci man fetur daga gobe, da tsadarsa da kuma hauhawar farashin kayan masarufi

Mai tanadi yayi tanadi jama’a, marassa imani da rashin tausayi zasu sake jefa al’ummar Nigeria cikin wani sabon mawuyacin hali, talakawa basu huce da takaicin cire tallafin man fetur ba, ga wannan kuma ta zo, hakika akwai makarkashiya a cikin wannan al’amari, ana yiwa shugaba Buhari yakin sunkuru da zagon kasa, kuma duk saboda siyasa

Allah Ka isar mana, Ka bamu mafita na alheri Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button