Uncategorized

Za a sayar da butar shayi naira miliyan arba’in da tara

Masu auna darajar kaya sun ce za a iya sayar da butar shayin ta China a kan £100,000
Za a iya sayar da wata butar shayi ta China wadda aka gano ta a kulle a wani garejin mota a kan kusan fam 100,000, wato fiye da naira miliyan arba’in da tara.
Butar shayin wacce ta shafe daruruwan shekaru ta wani ma’aikacin gine-gine ne a yankin Derbyshire, sai dai wasu rahotanni na cewa mai yiwuwa ta wani sarki na zamanin ce, a cewar kamfanin yin gwanjon kayayyaki na Hansons Auctioneers.
Sun yi kiyasin cewa za a iya sayar da ita a kan tsakanin fam 20,000 zuwa fam 40,000m sai dai wasu ‘yan kasar China da ke son sayenta za su iya biyan fiye da wannan adadi.
Mamallakin butar yana shirin aika wa da ita kantin da ke bayar da kyautar kaya.
Mutumin mai shekara 51, wanda ba ya so a bayyana sunansa, ya ce kakansa ne da ya zauna a lardin Asia lokacin Yakin Duniya na Biyu ya kawo musu butar mai tsawon santimita 15.

.
ASALIN HOTON,HANSONS
Bayanan hoto,

Kakan mutumin da ya mallakin butar, Ronald Wadsworth, ya samu lambar yabo ta yakin Burma
Ta kwashe shekara da shekaru a cikin kayan kwanukan mahaifiyarsa kodayake daga bisani an saka ta a wani akwati aka ajiye a gareji a garin Church Gresley da ke yankin Derbyshire.
Sai dai kullen da aka yi sakamakon korona ya ba da dama mai garejin ya bincika kayan da ke cikinsa a tsanake.
“Ina so na fadi gaskiya, mun so mu tura da dukkan kayan kantin da ke bayar da kaya kyauta,” in ji ta.
“Kodayaushe ina tunani kan butar shayin, wacce nake kallonta a matsayin wani abu na musamman.
“Duk da haka, da na kai ta Hansons ba ni da tabbaci, don haka na fito da wasu kayayyaki domin su yi musu daraja, kuma sun yi min dariya da na fasa sayar da butar.”

.
ASALIN HOTON,MARK LABAN/HANSONS
Sai dai masu auna darajar kayayyaki na Hansons sun bayyana cewa butar ta samo asali ne tun karni na 18 kuma mai yiwuwa Sarki Qianlong ya yi amfani da ita.
Charles Hanson, mai kamfanin auna darajar kayayyaki, ya ce akwai wasu butocin “masu kama da waccan” kuma dukkansu suna adane a gidajen adana kayayyaki na Taiwan da China.
Ya kara da cewa: “Wannan kullen shi ne mafi kyawu da ya faru a duniya. Abin al’ajabi ne yadda aka samu butar sarki a gidan da ke Derbyshire.”
Za a sayar da butar a baje-kolin da za a yi a shafin intanet ranar 24 ga watan Satumba, bbchausa na ruwaito
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA