Yan Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafara (IPOB) Sun Kashe Hausawa ‘Yan Arewa Mutum Biyu Tare Da Raunata Wasu Biyu A Jihar Ribas
.
….Kungiyar “Arewa Media Writers” tana kira ga Gwamnatin Nigeria da ta gaggauta nemo wa ‘yanda sukayi wannan ta’addacin tare da hukunta su.
Kamar yadda Jaridar Daily Trust dazu da safe ta wallafa wasu ‘yan kungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafara ta IPOB sun kaiwa Hausawa farmaki cikin ranakun Asabar da Lahadi a jihar Rives dauke da makamai inda ‘yan kungiyar suka kashe hausawa har mutum biyu tareda raunata wasu mutum biyu.
Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban Kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, tana takaici tare da bakin ciki kan wannan ta’addacin da kungiyar IPOB tayi kan ‘yan uwanmu ‘yan Arewa dake zaune a jihar Ribas, kuma tana Allah wadai da wannan ta’addacin.
Haka zalika kungiyar “Arewa Media Writers” ta na kira ga Gwamnatin Nigeria da ta tabbatar ta nemo wadanda sukai wannan ta’addacin tare da hukunta su domin dakatar da sake afkuwar haka a nan gaba.
Idan aka bari wannan abu ya ta tafi a haka to babu shakka wata dama ce suka samu don cigaba da aikata ta’addaci kan al’ummar yankin mu na Arewa, dake zaune a yankunan su, kuma kabilanci zai shiga ciki wanda munaga hakan bazai haifar mana, da ‘da mai ido ba.
Jinin dan Arewa yana da matukar muhimmanci a wajan Kungiyar “Arewa Media Writers”, don haka muna kara kira ga Gwamnatin Nigeria da Gwamnatin jihar Rives da su gaggauta nemo wa ‘yanda suka yi wannnan ta’addancin tare da yanke musu hukunci dai dai da abunda suka aikata, don ganin an dakatar da sake faruwar hakan anan gaba.