Labarai

Wata sabuwa ! Uwar gidan El-Rufai na son mace ta maye gurbin Sarkin Zazzau

Advertisment

Uwar gidan gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Isma El-Rufai ta roƙi mai gidanta da ya naɗa mace domin maye gurbin Sarkin Zazzau, wanda ya rasu a ranar Lahadi.
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, ta ce domin tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata, ta roƙi gwamnan kan cewa ko akwai yiwuwar a sake samun wata sarauniya a Masarautar Ta Zazzau kamar irin Sarauniya Amina?
Bbchausa ta kara da cewa, sai dai gwamnan bai amsa mata ba tukun kan wannan batu a halin yanzu, inda ko a jiya gwamnan ya ce ya duƙufa kan karanta littafin da wani Bature ya rubuta domin taimaka masa wajen yanke shawarar zaɓen sabon Sarkin Zazzau.

Sai dai mai gidanta gwaman El-rufai yace mutane su daina amfani da jita jita suyi amfani da labaran ingantattu domin sanin yadda al’amarin ke tafiya.

In the interest of gender equality, @elrufai Can we get another Queen Amina of Zazzau?

— Hadiza Isma El-Rufai (@hadizel) September 25, 2020

Advertisment
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button