Wata sabuwa: Annobar da ta lashe rayuka 200m a karni na 13 ta dawo a kasar China (Hotuna)
Kasar China ta sanar da barkewar wata annobar da tafi cutar Coronavirus illa
Cutar tana kashe mutum ne da zarar ta kamashi, kuma kwana daya takeyi ta kashe mutum
Wani yaro mai shekaru 3 da haihuwa, ya kamu da cuta da ake kira ‘Black Death’ a China
Likitoci sun tabbatar da barkewar mummunar cutar, dake kashe mutum cikin kankanin lokaci.
Wani yaro mai shekaru 3 da haihuwa ya kamu da mummunar cutar, wanda yanzu haka yana asibiti likitoci na kokarin ceto rayuwarsa. Yaron, dan wani kauye ne mai suna Menghai dake Yunnan.
kamar yadda Legithausa na ruwaito an tabbatar da yaron ya kamu da cutar mai kisan farat daya ranar Litinin, kamar yadda Chinese State Media ta sanar.
Annobar mai suna “Bubonic Plaugue” wata kwayar cuta ce wacce kwarin da ke zama inda beraye suke, suke yada wa. Tana kisa cikin kwana daya idan ba’a yi gaggawar kula ba.
Gwamnatin China ta fara zabura wurin bada taimakon gaggawa gudun kada wata cutar ta barke kamar yadda Cutar Covid-19 tayi.
An gano sabon al’amarin, tun bayan an tsinci wasu matattun beraye 3 da ke dauke da cutar a kauyen Menghai dake China.
Kamar yadda WHO ta bayyana, an taba samun barkewar irin wannan cutar ta ‘Black Death’ a karni na 14, inda har tayi sanadiyyar kashe mutane miliyan 200.
A wata kasa dake makwabtaka da China, mai suna Mongolia, an samu mutane 22 da ake zargin sun kamu da cutar, inda aka tabbatar da mutuwar mutum 6.
Legithausa sun kara da cewa an samu labarin wata mata mai shekaru 25 da aka kwantar a asibiti bayan ta ci wani bera mai dauke da cutar.
Farkon wannan watan, wani mutum mai shekaru 38 da haihuwa a Khovsgol ya kamu da cutar.
Kamar yadda aka gano, a karni na 13, ‘Black Death’ ta taba barkewa a nahiyar Turai da Asiya, inda har mutane miliyan 20 suka rasu. Hakan yayi sanadiyyar kashe 1/3 na yawan mutanen nahiyoyin tsakanin 1347-1352.