Labarai

Ton Dubu Talatin Na Masara Domin Yin Abincin Kaji, Yan Najeriya Basu Fahimci Manufar Gwamnati Buhari Ba

Fitar da Ton 30,000 domin sayarwa kamfanonin sarrafa abincin kaji alkairi ne wa talakawan Najeriya a daidai wannan lokaci da abun sanyawa a bakin salati ke kokarin fin karfin talaka, sai dai har yanzu da yawan mutanen mu basu fahimci alfanun yin hakan ba.

Kamfanonin sarrafa abincin kaji sun taimaka matuka gaya wajen hauhawan farashin masara wacce da ita talaka ke rayuwa, kusan duk inda masara take waɗannan kamfanoni suna bi suna sayeta da tsada, hakan ya sanya masarar tayi tashin goron zabo, fahimtar hakan da gwamnati tayi shi ya sanya ta ware waɗannan Ton na masara domin sayarwa kamfanonin cikin farashi mai rangome.

Yin hakan zai sanyasu kyale masarar dake hannun yan kasuwa, su kuma yan kasuwa masu burin sanya talaka cikin garari zasu rasa damar da suka samu na kaiwa kamfanoni masarar, sakamakon haka dole zasu fidda masarar domin sayarda ita akan farashin ta na farko.

Wannan tsari zai taimaka wajen faduwar farshin masarar, zai tilasta yan bakar kasuwa su fidda masarar da suka tara don sayarwa kamfani.

-Haji Shehu
5/Satumba/2020

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button