Labarai

Sojoji Sun Hallaka Gawurtaccen ‘Dan Ta’adda Terwase Akwaza Wanda Yafi shahara da suna Gana (Hotuna)

Advertisment

Jiya talata Allah Ya kawo karshen ajalin gawurtaccen ‘dan ta’adda Terwase Akwaza wanda yafi shahara da sunan Gana

Gana shine babban kwamandan shugaban kungiyoyin barayi a yankin jihohin Benue da Taraba, an ayyanashi cikin wadanda ake nema ruwa a jallo tun a shekarar 2016 bayan wani mummunan hari da ya haddasa mutuwar daruruwan mutane da jami’an tsaro, gwamnatin jihar Benue ta saka Naira miliyon 50 a matsayin tukwici ga duk wanda ya kawo labarin inda yake boye aka kashe shi ko aka kamashi

A cikin wannan lokaci sai Gwamnatin jihar Benue ta shirya tsarin yin afuwa ga wadanda suke ta’addanci a jihar domin a samu zaman lafiya, jiya talata da yamma Gana dashi da yaransa guda 172 sun kwaso makamansu zasu kawo wa gwamnatin jihar Benue domin a masa afuwa sai sojoji suka tareshi a hanya suka tafi dashi

Kwamandan sojoji rundina na 4 na Special Forces Command dake da sansani a garin Doma Brigadier General Maude Ali Gadzama ya tabbatar da cewa bayan sun tafi da Gana sun hallakashi har lahira

Advertisment

Yadda abin ya faru shine; Gana ya fito daga maboyarsa a jeji tare da yaransa guda 172 kai tsaye ya shiga garin Katsina-Ala inda ya bayyana tubansa a gaban manyan sarakunan gargajiya na kabilar Tiv da kuma Sarkin tsafi, yana kan hanyarsa na zuwa fadar gwamnatin Benue dake Makurdi da yammacin jiya talata domin ya mika makamansa sai sojoji suka tareshi suka tafi dashi suka hallakashi

Datti Assalafy ya cigaba da cewa kashe wannan kasurgumin ‘dan ta’adda da sojoji sukayi daidai ne, an taba yiwa Gana afuwa a shekarar 2015 amma ya sake komawa, don haka babu bukatar a kyaleshi ya sake yaudaran gwamnati, kashe shi da akayi daidai ne, hatta Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari ya jima yana nemansa, Abba Kyari ya taba yin wata guda cur a garin Benue yana neman Gana, ya shiga lunguna da sako da manyan dazuka da tsaunuka amma bai sameshi ba

Duk rikicin fulani makiyaya da manoma da yake faruwa a jihar Benue da Taraba Gana yana da hannu a ciki, hakanan duk wani garkuwa da mutane da fashi da makami Gaba yana da hannu a ciki, ya salwantar da rayukan mutane da ba zai kirgu ba, ni ina da fahimtar cewa da hannun Gwamnan Benue Samuel Ortom a kashe Gana da sojoji sukayi, tarko aka dana masa, kuma ya fada, jinjina gareku sojojin Nigeria

Hoto na farko fuskar Gana ne, hoto na biyu shine a shekarar 2015 lokacin da gwamnatin Benue ta masa afuwa ya mika mata makamansa, daga bisani yaci amanar gwamnatin ya koma ga ayyukansa na ta’addanci

Allah Ka tabbatar mana da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria, Ka mana maganin duk wani ‘dan ta’adda da yake tunanin ya gagara Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button