Labarai

Shin Ko Kun San Cewa Ba Hanan Bace Yar Autar Baba Buhari Ba ?

~Ga Asalin ‘yar Autar Shugaba Muhammadu Buhari..

Wato Jama’ar Nageriya da dama suna tunanin Hanan Buhari itace diyar Shugaba Buhari ta karshe last Born ko? To ba Haka bane, diyar Shugaba Buhari ta karshe itace NOOR (Amina Buhari) An haifeta A Shekara ta 2004, a ranar Sha hudu 14 ga watan Satumba lokacin mulkin Obasonjo, yanzu tana da shekaru 16 a Duniya,
Binciken M Inuwa MH ya tabbatar da cewa ita Noor Amina Buhari Ba’a cika bayyana fuskarta ba sai sunanta shiyasa Jama’a da dama Basu santa ba sai na kusa kusa da Shugaba Buhari ne Suka San asalin fuskarta, a ranar Ashirin da takwas 28 ga watan mayu din wannan shekara 2020 ne Zahra Buhari ta fara saka cikakken Hoton Noor (Amina Buhari) ta Kuma kirata da suna ‘yar Auta a shafinta na Instagram Shima Kuma ba tare da ta bayyana ko Wacce ba wasu da dama na tunanin Hanan ce sakamakon suna kama sosai saidai Hanan tafi Noor Haske, Zahra ta rubuta Cikin harshen turanci a shafin nata tana Mai cewa…

We all have that last Born, mummy still call her my baby lol,
Are you also the last baby?
What does your mum call you?
Inji Zahra Buhari

Ga Fassara, Baki dayanmu Muna da ‘yan auta, haryanzu mummy tana kiranta da baby, barkwanci)
Kaima dan auta ne?
Wanne suna mamanku take kiranka dashi?
Inji Zahra Buhari

Noor Amina Buhari ko a Hoton Family Ba’a cika  saka ta ba koma an sakata Basu so su ambaci sunanta sakamakon ana so a boye ta, ko account dinta na shafukan sada zumunta a kulle Suke Ba’a barin kowa ya shiga sai Wanda ita Noor din taso ya shiga ma’ana private account ne Hakan yasa fuskar ta take bakuwa ga Jama’a, sai dai wannan lokacin na Auren Hanan ta bayyana a hotunan bikin…

Bincikenmu ya Gaza gano Mana dalilin boye fuskar ta…

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button