Uncategorized
Shahararren Jarumin Bollywood Jaya Prakash Reddy Ya Rasu
Da safiyar talatar nan ne dai muka tashi da labarin mutuwar shahararren jarumin fina-finan Telugu na kasar India wato Jaya Prakash Reddy a gidan shi dake garin Guntur, yankin Andhra dake kasar ta India.
Arewamobile kamar yadda ta ruwaito,Prakash Reddy ya rasu yana da shekaru 74 a duniya sakamakon ciwo mai alaka da bugun zuciya. Reddy ya fara fitowa a film a shekarar 1988 inda bai fara haskawa sosai ba sai bayan shekara goma.
Prakash Reddy yafi yawan fitowa a matsayin boss a cikin fina-finan sa na shekarun baya. Sannan kuma yakan taka rawar barkwanci a cikin fina-finan shi na baya-bayan nan.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com